24 Yuli 2026 - 18:17
Source: ABNA24
Ofishin Jakadancin Iran A London: Siyasar "Kai Guda Ga Ido Guda" Ikirari Ne Ga Laifin Yaƙi

Ofishin Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a London, yayin da yake yin Allah wadai da maganganun Marco Rubio, Ministan Harkokin Wajen Amurka game da manufar Washington a kan Iran, ya sanar da cewa: Maganar "kai guda a kan ido guda" ikirari ne a fili na hare-haren marasa daidaito, da hukunta jama'a, da kuma niyyar aikata laifin yaƙi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Ofishin Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a London a ranar Juma'a, ta hanyar buga wani sako a shafin X, ta rubuta cewa bayanin manufar ta'addancin Amurka a kan Iran da kalmar "kai guda a kan ido guda," yana nuna tunanin masu laifi da niyyar jami'an Amurka na aikata laifin yaƙi.

A cikin wannan sako an ce: Ka'idar tarihi ta "ido a kan ido" an kafa ta ne daidai da manufar takaita ramuwar gayya da hana tsananta tashin hankali, kuma wannan tunanin shi ne tushen ka'idojin wajabci da daidaito a cikin dokokin duniya na zamani.

Ofishin Jakadancin Iran ya kara da cewa: A cikin dokokin duniya, kare tsarin " Ido guda, kai guda" yana nufin ikirari a fili na yin hare-haren da ba su da daidaito da hukunta gungun jama'a da kai hari a kan ababen more rayuwa da wuraren fararen hula, wanda ya saba wa ka'idodin dokokin duniya wanda shi ne laifin yaƙi karara.

Ofishin Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a London ya kara da cewa: Irin waɗannan maganganun hukuma, shaida ce kai tsaye ta niyya da sanin jami'an da suka ba da umarnin waɗannan ayyuka, kuma a aikace suna rubuta muhimman takardu game da alhakinsu a fayil din duniya na waɗannan laifuka.

A ƙarshen wannan sako an ce: Masu laifi bai kamata su tsira daga hukunci ba.

Marco Rubio, Ministan Harkokin Wajen Amurka, a baya, a martanin da ya mayar ga sakon Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda ya bayyana manufar tsaron ƙasar a matsayin "ido a kan ido," da wani salon wulakanci, ya yi iƙirarin cewa manufar Donald Trump shugaban Amurka ita ce "kai guda a kan ido guda."

Wannan yana faruwa ne a daidai lokacin da Amurka, tun daga ranar 7 ga Yuli 2026, biyo bayan wasu iƙirari game da kai hari a kan wasu jiragen ruwan da ke wucewa ta kudancin mashigar Hurmuz, ta fara wani sabon zagaye na ta'addancin soji a kan Iran, kuma a cikinsa, ta kai hari a kan gadoji, hanyoyin jirgin kasa, cibiyoyin ruwa, rumbunan alkama da sauran ababen more rayuwa na fararen hula.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta ɗauki waɗannan hare-hare a matsayin keta Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya a fili da kuma fahimtar juna game da kawo ƙarshen yaƙi, kuma ta jaddada cewa kai hari a kan ababen more rayuwa na jama'a da cibiyoyin fararen hula, laifin yaƙi ne.

Sayyid Abbas Araghchi, Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya jaddada cewa duk wani ta'addanci a kan Iran, ciki har da kai hari a kan ababen more rayuwa na ƙasar, za a fuskance shi da martani mai ƙarfi.

………………

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha