23 Yuli 2026 - 10:33
Source: ABNA24
Yadda Isra’ila Ke Asarar Makudan Kudaden Farfaganda A Amurka

Gwamnatin yahudawa, tun daga farkon yaƙin Gaza, ta kashe dubban miliyoyin daloli don tallace-tallace na dijital, ayyukan masu tasiri (influencers) da kamfanonin hulda da jama'a a Amurka.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Gwamnatin yahudawa, tun daga ranar 7 ga Oktoba 2023, ta zuba jari da ba a taɓa yin irinsa ba a cikin yaƙin gasar dijital, masu tasiri da kamfanonin hulda da jama'a a cikin Amurka. Wannan mataki sun yi shi ne da nufin hana dagula hoton wannan gwamnati a tsakanin masu ra'ayin mazan jiya, Kiristoci da matasan Amurka.

Amma alkaluman suna nuna sakamako mai karo da juna. Duk yadda injin tasirin gwamnatin yahudawa ya faɗaɗa, tausayawa ga Falasdinawa tsakanin Amurkawa ya ƙaru, goyon bayan gwamnatin yahudawa ya ragu, kuma bambance-bambance sun kai ga akwatunan kada kuri’un zabe da majalisar Amurka.

Ƙaruwar Kudaden Da Ba A Zata Ba

"Omar Ben Ya'akov," ɗan jaridan jaridar Ibrananci "Haaretz," ya ba da cikakken hoto game da girman waɗannan kudade. A cikin rahoton da ya buga a ranar 19 ga Yuli 2026, ya ƙiyasta alkawuran kuɗi da gwamnatin yahudawa ta yi don yaƙin neman zaɓe na waje tun daga farkon yaƙin a kusan dala miliyan 100.

Waɗannan kudade sun haɗa da yaƙin neman zaben yaudara daga ofishin talla na gwamnati da darajarsa ta kai shekel miliyan 174, wanda ya kai kusan dala miliyan 52. Daga wannan adadin, shekel miliyan 90 an kashe su a Google, shekel miliyan 60 a YouTube, shekel miliyan 10 a dandalin X, da shekel miliyan 14 a dandamali biyu na "Outbrain" da "Taboola."

Ben Ya'akov a cikin wani rahoto na baya da aka buga a ranar 18 ga Yuni, ya bayyana cewa gwamnatin yahudawa ta ƙara kasafin kuɗin yaƙin tallace-tallace da farfganda da ya shafi al'ummar Kiristocin Republican zuwa fiye da dala miliyan 40. Adadin da ya ninka kasafin farko sau uku. Haka kuma an kulla wata yarjejeniya ta kusan dala miliyan ɗaya don samarwa da kirkirar labari na dijital a New York.

Waɗannan ayyuka suna nuna samar da tsari na dogon lokaci don tasiri da kiyaye dangantakar gwamnatin yahudawa da jihar ra'ayin mazan jiya na siyasar Amurka.

Baya ga waɗannan kudade, shekel miliyan 25, wanda ya kai dala miliyan 8 da 165,000, an kashe su don kimanin ƙungiyoyi da masu tasiri 100, da shekel miliyan 20, wanda ya kai dala miliyan 6 da 532,640, an kashe su don samarwa da yada bidiyoyi kawai.

Haka kuma, kasafin kuɗin diflomasiyyar jama'a na gwamnatin yahudawa ya ƙaru daga shekel miliyan 545, wanda ya kai kusan dala miliyan 178 a shekara ta 2025, zuwa shekel biliyan 2.35, wanda ya kai kusan dala miliyan 730 a shekara ta 2026. Tabbas wannan kasafin kuɗi na duniya ne, kuma ba na Amurka kaɗai ba.

Akwai ci gaba…

………………………..

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha