15 Yuli 2026 - 00:21
Source: ABNA24
Iran: Gwamnati Ta Sanar Da Daga Taron Tunawa Da Imam Shahidi (Qs) Zuwa Lahadi Mai Zuwa

Gwamnatin Iran a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa an jinkirta lokacin gudanar da taron tunawa da Imam Shahidin Juyin Juya Hali Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i (Allah Ya tsarkake ruhinsa), wanda za a gudanar da shi a ƙarƙashin kulawar rassan gwamnati uku na ƙasar, zuwa ranar Lahadi mai zuwa (19 ga Yuli), da karfe 10 na safe.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: A cikin wannan sanarwar ya zo: "Muna sanar da al'ummar Iran mai daraja da girmama, cewa an jinkirta taron tunawa da Imam Shahidin Juyin Juya Hali (Allah Ya tsarkake ruhinsa), wanda gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta shirya yi gobe Laraba, zuwa ranar Lahadi (daidai 19 ga Yuli), da karfe 10 na safe."

Sanarwar ta kara da cewa: "Za a gudanar da wannan taron a ƙarƙashin kulawar rassan gwamnati uku na ƙasar, a babban filin sallah na Imam Khomeini (R.A) a Tehran".

……………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha