7 Yuli 2026 - 08:50
Source: ABNA24
An Gabatar Da Sallar Janaza Kan Gawa Mai Tsarki Ta Shahidin Jagoran Musulunci

Ayatullahil-Uzma Jawadi Amuli, ta hanyar halartarsa a masallacin Jamkaran mai tsarki, ya yi sallar jana'iza a kan gawar jagora shahidin juyin juya halin Musulunci.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA - An yi sallar jana'iza a kan gawar jagora shahidin Iran da 'yan iyalinsa, da safiyar yau Talata 7 ga Yuli, tare da jagorancin Ayatullahil-Uzma Abdullah Jawadi Amuli, tare da halartar miliyoyin masoya na al’ummomi da suke koyaushe a shirye a wurin haduwar masoya, masallacin Jamkaran mai tsarki.

Ayatullahil-Uzma Jawadi Amuli a taron sallar jana'iza a kan gawar "Jagora Shahidin Juyin Juya Hali," ya yi addu'o'i masu cike da baƙin ciki da ruhaniya, yana roƙon Allah Maɗaukaki Ya karɓi wannan shahidi mai daraja a cikin rahamarsa da kuma matsayin shahada.

Wannan babban marj’in koyi a cikin wani ɓangare na addu'o'insa, da murya mai cike da ruri da radadi da raurawa da baƙin ciki, ya yi addu'a kamar haka:

"اللهم إنه نزل مجاهداً موحداً"

"اللهم، اللهم، اللهم إنه نزل عندک شهیداً"

"اللهم إنه نزل عندک قتیلاً للإسلام، قتیلاً لأمةٍ مسلمة"

"Allahumma innahu nazala mujahidan muwahhidan"

"Ya Allah, lalle shi ya sauka a wurinka yana mai jihadi mai tauhidi".

"Allahumma, Allahumma, Allahumma innahu nazala 'indaka shahidan"

"Ya Allah, ya Allah, ya Allah, lalle shi ya sauka a wurinka yana mai shahada".

"Allahumma innahu nazala 'indaka qatilan lil-Islam, qatilan li-ummatin Muslimah"

"Ya Allah, lalle shi ya sauka a wurinka yana wanda aka kashe domin Musulunci, wanda aka kashe domin al'ummar Musulmai".

Waɗannan kalmomi, waɗanda suka kasance tare da tsananin tausayi da rurin Ayatullahil-Uzma Jawadi Amuli, sun sanya yanayin bikin ya zama mai ruhaniya da tasiri sosai, kuma sun sanya hawayen masu halarta zub. Manufar waɗannan addu'o'in tana nuna jihadi, tauhidi, ikhlasi da shahadar jagora shahidin juyin juya hali a tafarkin Musulunci da al'ummar Musulunci, kuma tana roƙon Allah Maɗaukaki Ya karɓi wannan mujahidin shahidin a cikin rahamarsa da karamcinsa.

…………………………….

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha