7 Yuli 2026 - 08:59
Source: ABNA24
An Fara Rakiyar Jana'izar Gawar Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali A Qom + Bidiyo

An fara jana'izar gawar Shahidin jagoran al'umma, da safiyar yau daga karfe 8 daga masallacin Jamkaran mai tsarki, kuma masu makoki sun fara rakiyar gawarsa zuwa haramin Hazrat Sayyidah Ma’asuma (S).

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA - An fara jana'izar gawar Shahidin Jagoran juyin juya hali, da safiyar yau da karfe takwas a birnin Qom. Wannan taron, wanda ya kasance tare da halartar dinbin miliyoyin Al’ummar Qom masu bin jagoranci da kishi, an fara shi daga masallacin Jamkaran mai tsarki, kuma taron masu makoki suna ci gaba da raka gawarsa zuwa haramin Hazrat Sayyidah Fatima Ma’asuma (S).

Titunan da ke kaiwa hanyar jana'izar sun cika da taron masu makoki, waɗanda tare da yin shelanta taken jarumtaka da waƙoƙin makoki, sun sake sabunta mubaya'a da manufofin juyin juya halin Musulunci. Za a kai gawar mai tsarki bayan wucewa ta hanyoyin da aka kayyade, zuwa haramin Uwar Gida Karimatu Ahlul Bayt As don yin bankwana na ƙarshe.

................

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha