Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Cibiyar Rundunar Sojojin Amurka a Yammacin Asiya da Arewacin Afirka (CENTCOM) a ranar Laraba a babban birnin Bahrain, tare da halartar wakilai daga kasashen Larabawa 11 na yankin CENTCOM, ta gudanar da taron tsaro-soji.
A cewar rahotanni Admiral "Brad Cooper," shugaban Cibiyar Rundunar Sojojin Amurka (CENTCOM), a ranar Laraba a birnin Manama na Bahrain, ya gana da manyan shugabannin soji na kasashe 11 na "Gabas ta Tsakiya" don tattaunawar tsaro ta yanki da ta ta'allaka kan hadin gwiwar tsaro da tsaron ruwa, kuma ya gudanar da taron tsaro na yanki na farko karkashin jagorancin Amurka tare da halartar jami'an soji na Siriya da Lebanon.
Waɗannan tattaunawar, waɗanda sojojin Bahrain suka karbi bakuncinsu, sun tattara jami'ai daga Bahrain, Masar, Jordan, Kuwait, Lebanon, Oman, Qatar, Saudiyya, Siriya, Hadaddiyar Daular Larabawa da gwamnatin yan aware da da Saudiyya ke tallafawa a Aden Yemen don tattauna yanayin tsaro na yanki da hanyoyin ƙarfafa hadin gwiwar soji.
A wannan taron, mahalarta sun jaddada kudurinsu na tabbatar da 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwan kasuwanci ta mashigar Hurmuz.
Cooper ya ce: "Muna ci gaba da tsayawa kafada da kafada tare da abokan huldarmu na yanki. Waɗannan tattaunawar sun jaddada kudurin hadin gwiwarmu ga tsaro da kwanciyar hankali na yanki."
Bahrain wurin da rundunar sojan ruwa ta Amurka ta biyar take a yankin. A lokacin yaƙin baya-bayan nan na Amurka da Isra'ila a kan Iran, hedkwatar rundunar ta biyar ta fuskanci hare-haren ramuwar gayya na sojojin Iran, kuma yawancin cibiyoyinta an lalata su.
Da alama Amurka tana ƙoƙarin, ta hanyar irin waɗannan tarurruka da daidaitawar tsaro-soji da kasashen yankin, ta kafa wata hanyar wucewa ga jiragen ruwan kasuwanci da dakon mai a yankin kudancin mashigar Hurmuz da kuma gabar tekun Oman da UAE. Hanyar da ba ta shafi ikon Iran a yankin arewacin mashigar Hurmuz ba.
Gwamnati da sojojin Iran sun bayyana cewa ƙirƙirar wata hanya ta daban a mashigar Hurmuz keta ce ga yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad, kuma Tehran ba za ta jure irin wannan abu ba.
Hedkwatar Khatamul-Anbiya a ranar Alhamis ta fitar da wata sanarwa wadda da alama martani ce ga taron da ya gabata na Manama, ta yi wa Amurka gargadin cewa duk wani tsoma baki da rawar kai a mashigar Hurmuz zai fuskanci martanin sojojin Iran.
……………………..
Your Comment