1 Yuli 2026 - 19:14
Source: ABNA24
Sharqil-Awsat: Tehran Tana Gab Da Gudanar Da Babbar Jana'izar Tarihin Iran

Wannan jaridar Saudiyya ta bayyana cewa ana gab da gudanar da jana'izar jagoran juyin juya halin Musulunci ne a daidai lokacin da Iran da Amurka ke da tsagaita wuta mai cike dA rauni bayan sanya hannu kan yarjejeniya ta farko don dakatar da yaƙi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Jaridar Saudiyya Al-SharqIl-Awsat a cikin wani rahoto game da shirye-shiryen ƙarshe na Tehran don gudanar da jana'izar gawar jagora shahidin juyin juya halin Musulunci, Shahid AyatullahIl-Uzma Khamene'i, ta rubuta: Ana sa ran mutane tsakanin 15 zuwa 20 miliyon za su halarci wannan babban taron.

Wannan jaridar ta rubuta: An kakkafe tare da girke Hotunan Shahid Ayatullahul-Uzma Khamene'i a babban filin sallah na Tehran, kuma jami'an aiwatarwa suna kammala shirye-shiryen ƙarshe na taron.

A rubutun Al-Sharqil-Awsat, wannan taron da aka jinkirta saboda abubuwan da suka faru na yaƙi, zai fara daga ranar Asabar, kuma za a kawo gawar jagoran Iran a filin sallah na Tehran tare da gawar ƴan iyalinsa.

Al-Sharqil-Awsat ta kuma yi nuni da hasashen halartar jama'a mai yawa, ta ba da rahoton ajiye matakan tsaro, aiki mai yawa na jami'an aiwatarwa, da shawarar kafofin yada labarai na Iran game da amfani da zirga-zirgar jama'a da kuma kula da ka'idojin lafiya a yanayin zafin rana.

Wannan jaridar ta ci gaba da yin nuni da rufe wasu cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu a Tehran da kuma sanya takaita zirga-zirga, ta kara da cewa: Bayan kammala taron a Tehran, za a tafi da gawar jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran zuwa Najaf da Karbala don gudanar da ayyuka na gaba, kuma a ƙarshe za a binne shi a Mashhad.

Wannan jaridar Saudiyya ta bayyana cewa ana gudanar da jana'izar jagoran juyin juya halin Musulunci ne a daidai lokacin da Iran da Amurka ke da tsagaita wuta mai rauni bayan sanya hannu kan yarjejeniya ta farko don dakatar da yaƙi.

…………………………….

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha