Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Yair Lapid, shugaban masu adawa a gwamnatin yahudawa, a cikin jawabinsa a majalisar wannan gwamnati (Knesset) ya ce Benjamin Netanyahu ta hanyar yi wa Amurkawa alkawarin rugujewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jawo su cikin yaƙi.
Lapid ya ce: Ni ma Kamar yawancin Isra'ilawa, na goyi bayan yaƙi da Iran amma ba zai yiwu a goyi bayan yadda ake tafiyar da shi ba.
Tsohon firayim ministan gwamnatin yahudawa, yana mai yin Allah wadai da aikin firayim ministan wannan gwamnati a yaƙi da Iran da kuma tashin hankali na baya-bayan nan da Amurka, ya ce: Netanyahu ya yi mana alkawarin babbar nasara ta tarihi.
Ya ci gaba da cewa: A maimakon haka, mun shiga cikin rikici da Amurkawa, an bude mashigar Hurmuz ga Iran, kudi sun kwarara zuwa ga dakarun juyin musulunci, makamai masu linzami na ballastic an harbo su ga Isra'ila, Hizbullah har yanzu tana cikin ma'aunin karfi.
Lapid ya sake mayar da martani don kare yaƙin da gwamnatin yahudawa ta yi wa Iran amma ya yi iƙirarin cewa: Netanyahu ya sha kaye har ma a cikin mafi saukin aikin diflomasiyya na tabbatar da Isra'ila a matsayin dimokuradiyya tana mai kare kanta daga mugunyar mulkin kama-karya na Musulunci mai tsattsauran ra'ayi da kyamar Yahudawa wanda ke ba da makamai ga ƙungiyoyin ta'adda a duk Gabas ta Tsakiya.
Shugaban 'yan adawar gwamnatin yahudawa, a jawabinsa na yau, ya yarda da rawar da firayim minista na yanzu ya taka wajen shigar da Amurka cikin yaƙi da Iran.
Lapid ya bayyana cewa: Ta yaya kuka kasa ma bayyana wannan yaƙi ga duniya? Netanyahu ya sayar wa Amurkawa wani labari da ya nuna cewa gwamnatin (Iran) za ta ruguje.
Ya kara da cewa: Bai fuskantar su ga kasadar hadari ba: ba ga tasirin kasuwannin makamashi ba, ba ga batun (mashigar) Hurmuz ba, ba ga Lebanon ba, kuma mafi muhimmanci ga wadannan batutuwa shi ne, bai kai ga riskar gaskiyar cewa shi da gaske bai san yadda zai kifar da gwamnatin (Iran) ba, kuma a lokacin da wannan shirin bai cimma ba, ya rasa amincinsu (Amurkawa) a tsakiyar yaƙi.
...........................
Your Comment