Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Ƙungiyar Larabawa ta yi kakkausar suka ga kutsawar da maziyartan Sahyuniyya masu tsattsauran ra'ayi suka yi wa Masallacin Al-Aqsa, wanda aka sanya karkashin kariyar sojojin mamaya na Isra'ila.
A cikin wata sanarwa ranar Talata, Sakatariyar Ƙungiyar Larabawa ta yi Allah wadai da kutsawar da maziyartan Sahyuniyya suka yi wa Masallacin Al-Aqsa, inda ta bayyana hakan a matsayin wulakanta wannan wuri mai tsarki da kuma kara tashin hankali mai haɗari wanda ke cutar da tunanin musulmai a duniya.
Sanarwar ta jaddada cewa waɗannan ayyuka suna wakiltar cin zarafi karara ga dokokin kasa da kasa da ka'idojin jin kai, da kuma lalata matsayin tarihi da shari'a na Masallacin Al-Aqsa.
Bugu da ƙari, Sakatariyar ta bayyana matukar damuwarta game da manufofin gwamnatin mamaya na ci gaba da takura wa masu ibada wajen hana su shiga Masallacin.
………………………………………….
Your Comment