Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Shugaban ƙasar Rasha, a wani taron bidiyo tare da takwaransa na Belarus da kwamandojin soji waɗanda suka halarci atisayen makaman nukiliya na farko na ƙasashen biyu, ya ce:
"Dole ne tsarin makaman nukiliya nuclear triad ya zama mai ba da tabbacin ikon mallakar ƙasa na Ƙungiyar Tarayyar Rasha da Belarus a tsakiyar tashin hankalin duniya da sabbin barazana.
Na faɗi haka a baya, kuma ina sake jaddadawa cewa yin amfani da makaman nukiliya mataki ne na ban mamaki kuma zaɓi ne na ƙarshe don tabbatar da tsaron ƙasashenmu."
Your Comment