Isra'ila Ta Kai Harin Bama-Bamai Mai Tsanani A Jabaliya

Isra’ila Na Ci Gaba Da Ayyukan Rusa Gine-Gine A Khan Yunis…Barna Mai Yawa A Zirin Gaza
19 Mayu 2026 - 12:28
Source: Almanar
Isra'ila Ta Kai Harin Bama-Bamai Mai Tsanani A Jabaliya

Dakarun Isra'ila sun kai hare-hare biyu ta sama a yammacin ranar Litinin a yankin Falouja a sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya da ke arewacin zirin Gaza, lamarin da ya haifar da barna mai yawa a gidaje da kewayen yankin, wanda a baya ya sha barna mai girma sakamakon ci gaba da yakin da ake yi a yankin.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: 'Yan jarida da majiyoyin yankin sun bayyana cewa hare-haren biyu sun afkawa wani gida da kewayensa a wani yanki mai cunkoso a sansanin Jabaliya, inda iyalai 'yan gudun hijira ke zaune a cikin gidajen da yake a lalace da tantuna da aka kafa a baraguzan gidajen da aka ruguje, har yanzu ba a samu asarar rayuka ba.

Majiyoyin sun ce sojojin mamaya sun bukaci wasu mazauna su tashi daga wani gida gaba daya kafin hare-haren, lamarin da ya janyo firgici tsakanin mazauna, musamman mata da yara, kafin a kai hare-haren ta saman a yankin.

A wani yanayi mai alaka da hakan, majiyoyin yankin sun bayar da rahoton jin karar fashe-fashe masu girma a Khan Yunis da ke kudancin yankin, sakamakon ayyukan rusa gine-gine da sojojin Isra'ila suka yi a ragowar gidaje da matsugunan da suka rage a yankunan da suke iko da su a gabashin birnin.

Wadannan abubuwan suna faruwa ne yayin da Isra'ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta, yayin da yanayin bil'adama ke ci gaba da tabarbarewa a cikin yankin, tare da karuwar adadin wadanda suka mutu da barnar da ta shafi ababen more rayuwa da kuma unguwannin zama.

....................................................

Your Comment

You are replying to: .
captcha