22 Mayu 2026 - 18:04
Source: ABNA24
Farmakin Ministan Harkokin Cikin Gidan Isra'ila Kan Ayarin Samoud Da Martanin Ƙasa Da Ƙasa

Ƙoƙarin Tel Aviv na tserewa daga abin kunyar da Ben Gvir yayi kan ayarin Samoud tare da goyon bayan Netanyahu ga fashin tekun da sojojin Isra'ila su kayi kan ayarin jiragen ruwan Sumoud da fargabar ministoci game allawadan duniya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sakamakon guguwar Allah wadai ta duniya game da nuna mugun halin da "Ben Gvir" ga masu fafutuka na "Ayarin Samoud ta duniya", jami'an sahayoniyawa sun yi kokarin kare gwamnatin Isra'ila daga kakkausar suka ta hanyar sukar da suka yi a fili ga lamarin; har ma ministan harkokin waje da wasu wakilan Knesset suka bayyana fitar da wadannan hotuna a matsayin babban rauni ga martabar Tel Aviv da kuma yunkurin neman karbuwa don samun jinjinawa.

Duk da haka, Netanyahu firaministan da ake nema ruwa a jallo a ICC yayin da yake bayar da goyon baya a fili ga wannan fashin da kuma fashin teku a cikin ruwan kasa da kasa, tare da kiran wannan rundunar ta lumana a matsayin "'yan ta'adda", ya yi iƙirarin cewa Tel Aviv na da hakkin toshe hanyar Gaza. Wannan ya sake nuna cewa dukkan bangarori daban-daban na wannan gwamnatin sun hada kai don ci gaba da aikata laifuka da kuma killacewa tare da ƙawanya ga Gaza.

A ɓangare guda kasashen Turai su hada kai kan sukar Isra'ila dangane da wannan lamarin in da suke da sammaci ga jakadun Tel Aviv tare da gargadarsu kan wannan lamari.

......................

Your Comment

You are replying to: .
captcha