21 Mayu 2026 - 22:53
Source: ABNA24
Iran Tana Sake Gina Ƙarfinta Na Soji Cikin Sauri

Rahoton leken asirin Amurka na nuna cewa Iran tana sake gina tushen masana'antun sojinta cikin sauri fiye da yadda ake zato, kuma ta ci gaba da samar da jiragen marasa matuki.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa:  "A cikin tsagaitawar mako shida da aka fara a farkon Afrilu, Iran ta ci gaba da wani sashi na samar da jiragen marasa matuki, wanda ke nuna cewa tana sake gina wasu daga cikin karfin sojinta da suka raunana saboda hare-haren Amurka da Isra'ila" – wannan yazo ne a wani bangare ne na rahoton CNN na yau bisa ga bayanin wasu majiyoyi biyu da suka san lamarin leken asirin Amurka.

A cewar wannan rahoton wanda ya dogara kan majiyoyi huɗu da suka san lamarin, "Sake gina karfin sojin, gami da maye gurbin wuraren makamai masu linzami da na'urorin harba su, da karfin samar da manyan makaman da aka lalata a lokacin yakin, yana nufin cewa idan Amurka ta ci gaba da kai hare-haren bama-bamai, Iran za ta kasance babbar barazana ga kawayen Washington a yankin”.

Your Comment

You are replying to: .
captcha