13 Mayu 2026 - 23:02
Source: ABNA24
Kuwait Ta Kai Hari Kan Jirgin Ruwan Da Kame Mutane Hudu

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Bait (ABNA) ya ruwaito cewa, Kuwait ta kai hari kan wani jirgin ruwan Iran a cikin Tekun Farisa tare da kama 'yan Iran 4, yayin da Iran ta bukaci a saki 'yan kasarta nan take. Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce Kuwait ta kai hari kan jirgin ruwan Iran tare da kama 'yan Iran 4 a cikin Tekun Farisa, in da yayi kira da a sake su nan take. A cikin bayaninsa, Abbas Araghchi ya ce wannan aikin da ya saba wa doka ya faru ne kusa da tsibirin da Amurka ke amfani da shi don kai hari kan Iran. Ya kuma ce suna bukatar a saki 'yan kasarsu nan take, ko su mayar da martani.

.........................................

Your Comment

You are replying to: .
captcha