8 Mayu 2026 - 23:41
Source: ABNA24
Takaitaccen Tarihin Da Ayyukan Kamfanin Nukliyar Rasha (Rosatom) Tun Kafawa Zuwa Yanzu

Rosatom, wanda kuma aka fi sani da State Atomic Energy Corporation Rosatom, babban kamfani ne mallakin gwamnatin Rasha da ke birnin Moscow, wanda ya kware a fannin makamashin nukiliya, kayayyakin da ba na makamashin nukiliya ba da kuma manyan kayayyakin fasaha na zamani.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): An kafa Rosatom ne a ranar 1 ga Disamba, 2007 bisa dokar da Shugaba Vladimir Putin ya sanya hannu. Ya maye gurbin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Tarayyar Rasha (Federal Agency on Atomic Energy).

1. Takaitaccen Tarihi

Tarihin kamfanin ya kafu ne tun zamanin Tarayyar Soviet, inda aka fara gudanar da ayyukan nukiliya a shekarar 1953. Daga baya aka canza masa suna zuwa Ma'aikatar Makamashin Nukiliya ta Tarayyar Rasha (MinAtom), sannan aka mai da shi Hukumar Tarayya a shekarar 2004, kafin a ƙirƙiro Rosatom a matsayin kamfani na gwamnati a shekarar 2007.

2. Girman Kamfanin

Kamfanin ya ƙunshi fiye da kamfanoni 350 da cibiyoyi, ciki har da cibiyoyin bincike na kimiyya, rukunin masana'antar makaman nukiliya, da kuma rundunar jiragen ruwa masu fasa kankara (icebreakers) ta duniya baki ɗaya. A cewar shafin yanar gizon kamfanin, Rosatom ya ƙunshi fiye da kamfanoni 550 kuma yana ɗaukar ma'aikata kusan 415,000 aiki.

3. Manyan Aiyukan Rosatom

Manyan ayyukan Kamfanin sun kasance kamar haka:

- Makamashin Nukiliya da Wutar Lantarki: Rosatom shi ne babban mai samar da wutar lantarki a Rasha, yana samar da 20.28% na jimillar wutar lantarkin ƙasar wanda ya kai terrawatt-hours 215.746 a shekara.

- Kasuwancin Duniya (Global Market Leadership): Shi ne kamfani na farko a duniya wajen yawan ayyukan gina tashoshin nukiliya a ƙasashen waje. A halin yanzu yana gina tashoshin nukiliya a ƙasashe kamar Turkiyya, Masar, Sin, Bangladesh, Hungary, Kazakhstan da sauransu.

- Sarkar Man Fetur (Nuclear Fuel Cycle): Shi ne kamfani tilo a duniya da ya mallaki dukkan fasahohin sarkar man fetur na nukiliya, tun daga hako Uranium zuwa sarrafa sharar nukiliya.

- Jiragen Ruwa da Kankara: Yana da rundunar jiragen ruwan nukiliya masu fasa kankara tilo a duniya, da kuma tashar wutar lantarki mai iyo tilo a duniya.

Matsayin Rosatom a Duniya (Global Ranking)

Wannan jeri yana nuna irin ƙarfin da Rosatom ke da shi a fannin nukiliya a duniya:

Shi ne aa 1 a duniya a yawan ayyukan gina tashoshin nukiliya a ƙasashen waje (inda ya gina cibiyoyi 41 a ƙasashe 11) sannan shi ne na 1 a duniya wajen inganta Uranium shi ne na 2 a duniya tace Arzikin Uranium shine na 3 a duniya wajen hako Uranium da samar da man fetur na nukiliya’ sannan shi ne Mai samar da 90% na Kasuwar gina tashoshin nukiliya a duniya

A taƙaice, Rosatom wani babban karfi ne a cikin gwamnatin Rasha. Yana da iko a kan dukkan ayyukan nukiliya na ƙasar, na zaman lafiya da na soji. Shi ne jagora a fagen samar da makamashin nukiliya, kuma yana taka rawa sosai a duniya wajen gina tashoshi da kuma samar da man fetur na nukiliya. Har ila yau, yana da alhakin cika alkawuran ƙasashen duniya na Rasha game da amfani da makamashin nukiliya cikin lumana da hana yaduwar makaman nukiliya.

Your Comment

You are replying to: .
captcha