Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A wasu ayyuka guda biyu daban-daban, mayakan Hizbullah na Lebanon sun yi amfani da jiragen sama marasa matuki sun hari wata tankar Merkava ta sahyoniya da wata tankar mai ɗauke da makamai ta Sojojin Isra'ila a Bint Jbeil. Sannan Hizbullah ta fitar da bidiyon yadda ta kai hari da jirgin maras matuƙi kan wani gungum sojojin Isra'ila a yankin Nimral-Jamal da ke kudancin Lebanon.
Sannan Hizbullah ta sake kai hari kan sabuwar Cibiyar Umurnin soji ta Sahayoniya wanda wannan hedikwatar sojojin Isra'ila da ke garin Al-Bayadh ba a dade da samar da ita ba amma ta fuskanci hari da wani jirgin maras matuki, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da kuma barna da dayawa. Sannan Hizbullah ta fitar da bidiyon hare-haren manyan bindigu kan dakarun mamaya a kudancin garin Al-Bayadah na kudancin Lebanon. Sannan Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bayyana a cikin wasu bayanai guda biyu cewa ta kai hari kan wani sojan sahyoniyawa da wata motar soji ta sojojin mamaya a safiyar yau kuma harin ya haifar da asarar rayuka da raunuka.
Your Comment