24 Afirilu 2026 - 22:32
Source: ABNA24
Yahudawan Orthodox A Zanga-zangarsu Sun Ƙona Tutocin Isra'ila 

Yahudawan Orthodox a bikin cika shekaru 78 da kafa Isra'ila a unguwar Mia Shirim da ke yammacin Kudus sun kona tutocin Isra'ila. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wataƙila kuna mamakin dalilin da yasa wasu Yahudawa a Isra'ila suka ƙone tutar Isra'ila! Dalilin wadannan zanga-zangar shi ne Yahudawan Orthodox (Harids), wanda suke adawa ta addinin Sahyoniyawa da kafa kasar Isra'ila. Ga waɗannan ƙungiyoyi, kafa ƙasar Yahudawa dole ne ya kasance a hannun Annabi Isa a lokacin zuwansa, ba ta hanyar siyasar ɗan adam ba, in ba haka ba yin hakan ba nufin yin shishshigi cikin aikin Allah! Sun nuna adawarsu ga gwamnati da kona tuta a bikin ranar samun 'yancin kai wanda suke ganin ya saba wa koyarwar addini.

Ana ganin wadannan zanga-zangar musamman a ranar samun 'yancin kai na Isra'ila, inda wasu daga cikin wadannan kungiyoyi suka kona tutar Isra'ila.

Your Comment

You are replying to: .
captcha