14 Afirilu 2026 - 17:03
Source: ABNA24
Dakarun Hizbullah Na Ci Gaba Da Arangama Mai Tsanani Da Sojojin Isra'ila + Bidiyoyi

Hizbullah ta shammaci Isra'ila da harba jirgin maras matuƙi da ke ɗauke da tsarin na'urar gani da bincike tare da bibiya da baza a iya ganinsa ba a karon farko.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Tashar Isra'ila ta 11 ta ba da rahoton cewa, a karon farko kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta harba jirgi mara matuki mai dauke da tsarin hasken wuta wanda ke da wahalar ganowa a kan dakarun Isra'ila. Sojojin Nasrallah sun yi arangama gaba da gaba da sojojin gwamnatin mamaya inda gidan rediyon sojojin Isra'ila suka bayar da rahoton cewa sojoji 10 na Bataliya ta 101 ta Paratrooper sun jikkata a wannan yaƙin na gaba da gaba da mayakan Hizbullah a kudancin Lebanon.

Rahoton ya ce an yi arangama ne a yankin Bint Jbeil, wanda a halin yanzu shi ne babbar cibiyar rikicin sojojin Isra'ila a kudancin Lebanon, in ji rahoton. Har walayau gidan rediyon sojojin Isra'ila ya kara da cewa, jami'an tsaro sun yi arangama da mayakan kungiyar Hizbullah a kusa da kusa da kuma musayar wuta.

Kafofin yada labarai na Isra'ila: Sojoji 10 ne suka jikkata a fadan uku daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali. Hizbullah ta harba jirgi mara matuki kan kayayyakin sojin Isra'ila sannan Hizbullah ta sanar da cewa ta kai hari kan wata motar Hummer ta sojojin Isra'ila a garin Ain Abel da ke kudancin Lebanon da kan wata motar sojojin Isra'ila a garin Kriat Shamuneh tare da Jiragen ƙunar baƙin wake guda biyu.

An kunna ƙararrawar gargadi a arewacin Falasdinu kamar yadda Majiyoyin labarai suka ba da rahoton kunna siren gargadi a cikin matsugunan sahyoniya na "Mesgaoam" da "Kriat Shammoneh" a arewacin Falasdinu bayan harin Hizbullah.

Sannan Hizbullah ta karkabo jirgin yaƙin F16 na Amurka kamar yadda ya ke anan ƙasa. Wannan jirgin an kakkaɓo a kwanakin da suka gabata bayan Hizbullahi ta harbe shi a arewacin yankunan da aka mamaye.

Sannan Hizbullah ta harbo wani jirgin saman yaƙi mara matuki nau'in Hirmus 450 da makami mai linzami.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha