Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA: Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, an wallafa sakon farko na Hazrat Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci.
Ga rubutun sakon kamar haka:
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
مَا نَنسَخْ مِنْ ءَآیَةٍ أَوْ نُنسِهَا نَأتِ بِخَیْرٍ مِّنْهَآ اَوْ مِثْلِها.
اَلسَّلامُعَلَیکَ یا داعِیَاللهِ وَ رَبّانِیَّ آیاتِهِ، اَلسَّلامُعَلَیکَ یا بابَاللهِ وَ دَیّانَ دینِهِ، اَلسَّلامُعَلیکَ یا خَلیفَةَاللهِ و ناصِرَ حَقِّهِ، اَلسَّلامُعَلیکَ یا حُجَّةَاللهِ وَ دَلیلَ اِرادَتِه؛ اَلسَّلامُعَلیکَ اَیُّهَا المُقَدَّمُ المَأمُول؛ اَلسَّلامُعَلیکَ بِجَوامِعِ السَّلام؛ اَلسّلامُعَلیکَ یا مَولایَ صاحِبَ الزَّمان.
A farkon maganata ya wajaba in miƙa ta’aziyyata ga Ubangidana – Allah ya gaggauta bayyanarsa – saboda shahadar mai girma Jagoran juyin juya hali, Khamenei mai hikima, kuma ina roƙon Ubangiji ta hannunsa ya yi wa al’ummar Iran mai girma ɗaya bayan ɗaya, har ma da dukkan musulmin duniya, da duk masu hidima ga Musulunci da juyin juya hali, da masu sadaukarwa da iyalan shahidan wannan tafiya ta Musulunci, musamman na wannan yaƙin na baya‑bayan nan, da kuma ni bawan Allah maƙasƙanci, addu’ar alheri.
Sashe na biyu na maganata yana ga babbar al’ummar Iran. Da farko dole ne in bayyana a takaice matsayata dangane da ƙuri’ar (zaɓen) Majalisar Kwararru. Ni wannan bawan mai hidima gare ku Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei, kamar ku, ta hanyar gidan talabijin na Jamhuriyar Musulunci na Iran na samu labarin sakamakon ƙuri’ar Majalisar Kwararru. A gare ni zama a wurin da kujerar shugabanci take, wacce manyan shugabanni biyu masu girma – Imam Khumaini mai girma da shahidi Khamenei – suka zauna a kanta, aiki ne mai matuƙar wahala. Domin wannan kujera tana da tarihin zama na wanda bayan sama da shekaru sittin na jihadi a tafarkin Allah, da barin nau’o’in jin daɗi da hutawa, ya zama lu’u‑lu’u mai haske da fuska ta musamman ba kawai a wannan zamani ba har ma a cikin tarihin shugabannin wannan ƙasa. Rayuwarsa da irin mutuwarsa sun kasance cike da daraja da ɗaukaka sakamakon dogaro ga gaskiya.
Na sami wannan sa’a ta ganin gangar jikinsa bayan shahadarsa; abin da na gani dutse ne na jarumta, kuma na ji cewa hannunsa mai lafiya ya kasance a dunkule. Game da fannoni daban‑daban na halayensa, masana dole ne su yi magana na dogon lokaci. A wannan lokaci zan takaita da wannan taƙaitaccen bayani, cikakkun bayanai kuma zan bar su ga lokuta da suka dace a gaba. Wannan shi ne dalilin da ya sa zama a kujerar jagoranci bayan irin wannan mutum yake da wahala; cike wannan tazara ba zai yiwu ba sai da taimakon Ubangiji da kuma goyon bayan ku jama’a.
A gaba ina so in jaddada wani muhimmin abu da ke da alaƙa kai tsaye da jigon maganata. Wannan shi ne cewa daga cikin fasahohin jagoran shahidi da kuma babban magabacinsa akwai shigar da jama’a cikin dukkan fannoni, da kuma fahimtar da su da wayar da kai a kai a kai, sannan a aikace su dogara da ƙarfinsu. Ta haka suka aiwatar da ainihin ma’anar “jamhuriya” da “jama’a”, kuma sun yi imani da hakan daga kasan zuciya. A cikin ‘yan kwanakin nan da ƙasar ta kasance ba tare da jagora da kwamandan rundunar sojoji ba, an ga tasirin wannan. Hikima da wayon al’ummar Iran a wannan lamari na baya‑bayan nan da jajircewa da jarumtarsu da kasancewarsu a fage sun sa abokai (masoya) suka yaba, makiya kuma suka yi mamaki. Ku ne jama’a kuka jagoranci ƙasa kuma kuka tabbatar da ƙarfinta.
Ayar da na kawo a farkon wannan rubutu tana nufin cewa babu wata aya daga ayoyin Allah da za a soke ko a manta da ita face sai Allah ya kawo mafi alheri daga gare ta ko makamancinta.
Dalilin amfani da wannan aya ba wai don na ɗauki kaina daidai da jagoran shahidi ba balle in ɗauka na fi shi; sai dai don in jaddada muhimmiyar rawar da ku jama’a kuke takawa. Idan aka karɓe mana wannan babbar ni’ima, Allah ya ba mu a madadinta, sake bayyana halartar ku jama’a kamar Ammar wajen kare wannan tsarin. Ku sani da ƙarfinku bai bayyana a fage ba, ba jagoranci ba kuma ba wata hukuma da aikinta shi ne hidima ga jama’a da za ta iya yin aiki yadda ya kamata. Domin wannan ya tabbata dole ne a fara da tuna Allah Madaukaki, da dogaro gare Shi, da kuma tawassuli ga tsarkakan Ahlul Baiti – tsira da amincin Allah su tabbata a gare su – kamar wani babban sinadari mai tabbatar da nasarori da buɗe kofofi iri‑iri. Wannan babbar ni’ima ce da ku kuke da ita, makiyanku kuma ba su da ita.
Na biyu, dole ne a kiyaye haɗin kai tsakanin dukkan sassan al’umma wanda yawanci yake bayyana musamman a lokutan wahala. Za a samu wannan ta hanyar kaucewa abubuwan da ke haifar da sabani.
Na uku, dole ne a ci gaba da kasancewa a fage cikin tasiri; ko dai kamar yadda kuka nuna a waɗannan kwanaki da daren yaƙi, ko kuma ta hanyoyin taka rawa a fannoni daban‑daban na zamantakewa, siyasa, tarbiyya, al’adu har ma da tsaro. Muhimmi shi ne a fahimci rawar da ta dace ba tare da lalata haɗin kan al’umma ba, sannan a aiwatar da ita gwargwadon iko. Daga cikin ayyukan Jagora da wasu jami’ai masu mas'uliyya akwai tunatar da jama’a ko wasu rukuni daga cikin al’umma game da wasu daga cikin waɗannan matsayar. Saboda haka ina jaddada muhimmancin halartar bukukuwan ranar Quds ta shekarar 1447, inda dole ne a ba da muhimmanci ga siffar karya ƙarfin makiya.
Na huɗu, kada ku yi sakaci wajen taimakon juna. Alhamdulillah wannan halayya ce ta yawancin Iraniyawa, kuma ana sa ran a cikin waɗannan kwanaki na musamman – da a dabi’a wasu daga cikin jama’a suke fuskantar wahala fiye da wasu – wannan zai fi bayyana. A nan kuma ina roƙon cibiyoyin hidima su ba da duk wani taimako ga waɗannan ‘yan ƙasa da kuma tsarin agajin jama’a ba tare da jinkiri ba.
Idan aka kiyaye waɗannan abubuwa, hanyar kaiwa ga kwanakin girma da ɗaukaka za ta buɗe a gare ku al’umma masu girma. Mafi kusa daga cikinsu, insha Allah, shi ne nasara a kan maƙiya a wannan yaƙin na yanzu.
Sashe na uku na maganata shi ne godiya ta musamman ga jaruman sojojinmu waɗanda a cikin yanayin da ƙasarmu da al’ummarmu suka fuskanci zalunci daga shugabannin rundunar girman kai na duniya, suka toshe hanyar makiya da duka masu ƙarfi kuma suka cire musu tunanin cewa za su iya mamaye ƙasarmu ko ma su raba ta.
Ya ku ‘yan uwa mayaƙa! Bukatar jama’a ita ce ci gaba da kare ƙasa ta hanyar da za ta sa maƙiya su yi nadama. Haka kuma babu shakka dole ne a ci gaba da amfani da matakin rufe mashigin Hormuz. Hakanan an yi nazari kan buɗe wasu sabbin fagage da maƙiya ba su da kwarewa a cikinsu kuma suke da rauni sosai; za a iya kunna su idan yaƙi ya ci gaba, bisa la’akari da maslahar da ta dace.
Har ila yau ina miƙa godiya ga mayaƙan rundunonin muƙawama. Muna kallon ƙasashen rundunonin muƙawama a matsayin mafi kyawun abokanmu, kuma muƙawama da rundunonin muƙawama wani bangare ne da ba za a raba su da ƙimar juyin juya halin Musulunci ba. Babu shakka haɗin kai tsakanin sassan wannan muƙawama zai rage tsawon lokacin tsira daga fitinar sahyoniya; kamar yadda muka gani Yemen mai jarumta da imani bata daina kare al’ummar Gaza ba, Hizbullah mai sadaukarwa ma duk da dukkan matsaloli ta taimaki Jamhuriyar Musulunci, haka kuma muƙawamar Iraki ma cikin jarumta ta bi wannan hanya.
Sashe na huɗu na maganata na ga waɗanda suka sami kowane irin nau’in rauni a cikin ‘yan kwanakin nan; kama daga waɗanda suka rasa wani masoyi ta hanyar shahada, ko waɗanda suka ji rauni, ko kuma waɗanda gidajensu ko wuraren kasuwancinsu suka lalace. Da farko ina bayyana cikakkiyar ta’aziyyata ga iyalan shahidai masu daraja.
Wannan bisa wata ƙwarewar rayuwa ce da na raba da su; ban da mahaifina wanda rasuwarsa ta zama ta kowa, na rasa matata mai ƙauna da aminci wacce nake da manyan fata a kanta, da kuma ‘yar uwata mai sadaukarwa wacce ta sadaukar da kanta wajen hidima ga iyayenta har ta samu ladan ta, da kuma ɗanta ƙarami, da kuma mijin wata ‘yar uwar tawa wanda mutum ne mai ilimi da daraja – duk sun shiga cikin jerin shahidai. Amma abin da ke sa juriya a kan bala’i ta yiwu har ma ya zama mai sauƙi shi ne tunawa da tabbataccen alkawarin Allah ga masu haƙuri na lada mai girma. Saboda haka dole ne a yi haƙuri kuma a dogara da taimakon Allah.
Na biyu, ina ba kowa tabbacin cewa ba za mu yi watsi da ramuwar jinanen shahidanku ba. Wannan ramuwar ba ta shafi shahadar jagoran juyin juya hali kaɗai ba; duk wani ɗan ƙasa da maƙiya suka kashe shi kansa lamari ne mai zaman kansa a cikin wannan fayil na ramuwar gayya. Wani ɓangare kaɗan na wannan ramuwa ya riga ya faru a zahiri, amma har sai an kai ga cikakken matsayi, wannan fayil zai kasance a kan sauran fayiloli; musamman game da jinin yara da ƙanananmu za mu fi nuna ƙwarin hankali. Don haka laifin da maƙiya suka aikata da gangan a makarantar Shajarat Tayyiba ta Minab da wasu makamantan lamura suna da muhimmanci na musamman a wannan ramuko.
Na uku, dole ne waɗanda suka ji rauni a waɗannan hare‑haren su samu kulawar lafiya da ta dace kyauta kuma su amfana da wasu fa’idodi.
Na huɗu, gwargwadon yadda yanayin yanzu ya ba da dama, dole ne a aiwatar da shirye‑shirye masu ma’ana domin diyya ga asarar kuɗi da aka yi wa gidaje da dukiyoyin mutane. Wadannan abubuwa biyu na ƙarshe wajibi ne ga jami’an da suka dace su aiwatar da su kuma su ba ni rahoto.
Abin da ya kamata in jaddada shi ne cewa ta kowace hanya za mu karɓi diyya daga maƙiya; idan suka ƙi, za mu ɗauka daga dukiyoyinsu gwargwadon yadda muka ga ya dace, kuma idan hakan bai yiwu ba za mu lalata dukiyoyinsu gwargwadon wannan adadi.
Sashe na biyar na maganata yana ga shugabanni da manyan masu tasiri a wasu ƙasashen yankin. Muna da maƙwabta goma sha biyar ta ƙasa ko ta ruwa, kuma koyaushe muna son kyakkyawar hulɗa da su. Amma maƙiya tun shekaru da dama suna gina sansanoni na soja da na kuɗi a wasu daga cikin waɗannan ƙasashe domin tabbatar da iko a yankin. A hare‑haren baya‑bayan nan, an yi amfani da wasu sansanonin soja, don haka kamar yadda muka yi gargaɗi a sarari – ba tare da kai hari ga waɗannan ƙasashe ba – mun kai hari ga waɗannan sansanonin kawai. Daga yanzu idan ya zama dole za mu ci gaba da yin hakan; duk da haka muna ci gaba da yin imani da muhimmancin abota da maƙwabtanmu. Wadannan ƙasashe dole ne su fayyace matsayarsu game da masu kai hari ga ƙasarmu da masu kashe al’ummarmu. Ina ba su shawara su rufe waɗannan sansanoni da wuri; domin ya kamata su riga su fahimci cewa ikirarin Amurka na kawo tsaro da zaman lafiya ƙarya ne.
Hakan zai sa su ƙara kusanci da al’ummarsu waɗanda galibi ba su yarda da haɗin kai da rundunonin kafirci da kuma halin wulakanci da suke nuna musu ba, kuma hakan zai ƙara musu ƙarfi da arziki. Ina sake jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ba tare da neman wani nau’in mulkin mallaka a yankin ba, tana shirye don haɗin kai da kyakkyawar hulɗa da dukkan maƙwabta.
A sashe na shida na maganata, ina magana da jagoranmu shahidi. Ya kai jagora! Tare da tafiyarka ka bar babban baƙin ciki a zukatan kowa. Ka kasance kana marmarin wannan ƙarshe har Allah ya ba ka shi a lokacin da kake karanta Alƙur’ani a safiyar rana ta goma ga watan Ramadan mai alfarma. Ka jure zalunci da yawa cikin ƙarfin hali da haƙuri ba tare da nuna damuwa ba. Mutane da yawa ba su san darajarka ta gaskiya ba, kuma watakila lokaci mai tsawo zai shuɗe kafin a kawar da shingaye da ke hana a gane wasu daga cikin bangarorinka.
Muna fatan daga matsayinka na kusanci da tsarkakan waliyyai, shahidai da salihai, ka ci gaba da tunanin ci gaban wannan al’umma da dukkan al’ummomin rundunonin muƙawama kuma ka roƙa musu alheri; kamar yadda ka kasance a rayuwarka.
Muna yi maka alkawari cewa za mu yi duk abin da za mu iya domin ɗaukaka wannan tutar – tutar gaskiya – da kuma cimma manufofinka masu tsarki.
A sashe na bakwai ina gode wa duk waɗanda suka ba ni goyon baya, ciki har da manyan maraji’ai na taqlid da manyan mutane daga fannoni daban‑daban na al’adu, siyasa da zamantakewa, da kuma jama’a da suka halarci taruka masu girma domin sabunta mubaya’a ga tsarin. Haka kuma ina gode wa shugabannin rassa uku na gwamnati da majalisar wucin gadi ta jagoranci saboda kyakkyawan shiri da matakan da suka ɗauka.
Ina fatan rahamar Allah ta musamman a cikin waɗannan sa’o’i da kwanaki masu albarka ta sauka ga al’ummar Iran har ma da dukkan musulmi da masu rauni a duniya.
A ƙarshe ina roƙon Ubangidanmu – Allah ya gaggauta bayyanarsa – a cikin ragowar dararen Lailatul Qadr da kwanakin watan Ramadan, ya roƙi Allah ya ba al’ummarmu cikakkiyar nasara a kan makiya, ya ba su ɗaukaka, yalwa da lafiya, kuma ya ba wa mamatan su matsayi mai girma a lahira.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu
Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei
21 Esfand 1404
22 Ramadan 1447
Your Comment