Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): An nada sabon jagoran juyin juya halin Musulunci bisa tabbatarwar majalisar kwararru, kuma Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei ya zama jagora na uku na tsarin Musulunci na Iran.
Nassin bayanin sakatariyar majalissar masana kwararru a wannan bangaren yazo kamar haka:
بسم الله الرحمن الرحیم
Da sunan Allah, mafi rahama, mai jinkai,
Al’umma mai daraja da 'yanci t Iran din Musulunci, Tsira da aminci Allah su tabbata a gare ku.
Majalisar kwararru, yayin da take mika ta'aziyya ga shahadar babban jagora Sayyid Ayatullahi Imam Khamenei (Qs), da sauran shahidai masu daraja, musamman kwamandojin rundunar soji da daliban Makarantar Shajreh Tayyeba a cikin garin Minab.
Tare da yin Allawadai ga Mummunan keta iyaka da Amurka da mugunyar tsarin Sahyuniyanci ba tare da bata lokaci ba bayan labarin shahada da daukakar ruhin jagoran juyin juya halin Musulunci zuwa rahamar ubanagiji, duk da tsananin yanayin yaki da barazana kai tsaye daga makiya a kan wannan babbar cibiyar da kuma Harin bam a sakatariyar majalissar kwararru. Hakan ya haifar da shahadar ma’aikata da dama da kuma jami’an tsaro na wannan rukunin, ba su yi jinkiri ba na dan wani lokaci a cikin tsarin zabar da gabatar da jagoran tsarin Musulunci kuma bisa ga ayyukan da ke cikin kundin tsarin mulki da ka’idojin cikin gida na Majalisar Kwararru, sun sanya matakan da suka dace da tsare-tsare yadda ya dace don gudanar da wannan taro mai matukar muhimmanci don gbatar da sabon jagora.
Don haka, an yi tsare-tsare da suka dace da tuntuba da ake bukata da suka dace don gudanar da taron manyan ƴan majalisar da suka halarta a duk sassan ƙasar ta yadda duk da tanadin doka ta sashe na 111 na kundin tsarin mulki na kafa majalisar wucin gadi, don kar ƙasar ta yi fama da matsalar shugabanci.
Majalisar kwararrun jagoranci, ta hanyar girmama babban matsayi na Wilayatul Faqih a lokacin rashin Sayyid Waliyil Asr (Allah ya gaggauta bayyanarsa) da mahimmancin batun shugabanci a Jamhuriyar Musulunci, ta lura da shekaru 47 da suka gabata na jagoranci mai hikima bisa ka'idar mutunci, 'yancin kai da ikon limaman juyin juya hali. Bisa tunawa da waɗancan shugabanni na Allah da mutane ta sanar da cewa wannan majalisa, bayan bincike mai zurfi da nazari mai zurfi tare da yin amfani da damar doka ta ashirin da 108 na Kundin Tsarin Mulki, wanda yayi daidai da nauyi na shari’a da imani da kasancewa a hadarar Allah Maɗaukakin Sarki, a wannan taro mai muhimmanci na yau Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamenei (Allah yak are shi) bisa kada kuri na wakilan Majalisar Kwararru sun zabe shi da gabatar da shi a matsayin jagora na uku na tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A karshe, tare godiya da girmamawa ga mambobin majalisar wucin gadi a Mataki na 111 na kundin tsarin mulki, ta gayyaci al'ummar Iran masu daraja, musamman masu fada aji da masana na makarantar hauza da jami'a, da su yi mubaya'a ga jagoranci da kuma kare hadin kai a akan fagen Wilayat. Muna rokon a fadar ubangiji ci gaban tausayawar Ubangiji madaukakin sarki ga wannan kasar da babbar al’ummarta.
Wassalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu
Majalisar Kwararrun Jagoranci
12/17/1404.
☫ Sakatariyar Majalisar Kwararru
..................................................
Your Comment