Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Makamin makami mai linzami da ke da nisan kilomita 1450 yana da ikon yin tafiya har sai ya kai hari da ga hadafinsa. A gungun makamai da suka gabata sun kasance mafi girman makaman da aka samu hadafinsu sakamakon raunin radar da tsarin tsaro na abokan gaba sahyoniyawa-Amurka, waɗannan makamai masu linzami sun fi kai hari cikin sauƙi a cikin 'yan kwanakin nan.
Cikakkun bayanai game da harba ayarin makamai karo na 28 tare da ramzi mai albarka na “Ya Amiral-Mu'minin (AS)” sun sauka kan hadafofi da manufofin Amurka da sahyoniyawa. Makamai masu linzami na Iran da jirage marasa matuka sun afkawa abubuwan more rayuwa na sansanin Al-Azraq, wanda ya kasance a matsayin sansani mafi girma kuma mafi yawan aikin kai farmaki na Amurka, Iran ta kai hari kan wannan sansani sau da dama. Hakanan kuma ta kai hari kan wuraren sojoji a Tel Aviv da Beer Assaba a cikin yankunan da aka mamaye da makamai masu linzami na "Khaibar" tare da manyan kawukan yaki masu nauyi.
Za a bunkasa girma da zurfin hare-haren dakarun sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin sa'o'i da kwanaki masu zuwa biyo bayan keta iyaka da sojojin Amurka da na sahyoniyawa su ke yi a kan Iran, kuma za a isar da nasarorin da ta samu ga kunnuwan masu daraja na al'ummar Iran.
Your Comment