6 Maris 2026 - 21:21
Source: ABNA24
Ƙasƙantar Amurka A Tekun Farisa

Amurka Ta Sha Kaye Tun Daga Samar Da "Rakiyar Jiragen Dakon Mai" Zuwa "Tserewa Daga Yankin".

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cikin wani ci gaba da sauyi da ba a taba ganin irinsa ba, sojojin ruwan Amurka sun yi watsi da ikon manyan sassan yankunan Tekun Fasha da Tekun Oman inda suka gudu suka barwa Rundunar kare juyin juya halin Musulunci.

Sabanin alkawuran da Donald Trump ya yi na samar da tsaron"rakiyar da jiragen ruwa masu dakon mai ƙarƙashin ikon jiragen ruwan Amurka" sai dai saɓanin hakan an samu hotunan tauraron dan adam da rahotanni yanzu sun nuna jiragen ruwan Amurka suna tserewa a zuwa wuri mai nisa tare da barin tankunan ajiyar mai a tashar jiragen ruwa. 

Jirgin USS Abraham Lincoln, wanda aka sanya a matsayin mai bada kariya ga manyan jiragen yakinta guda 90 da jiragen ruwa don tabbatar da tsaron makamashi da kuma fitar da mai daga yankin, a yanzu ya tsere da nisan kilomita 1,000 daga gabar tekun Iran kusa da Oman. 

Wannan nisa ba don motsa jiki ko nuna ƙarfi da shiri ba ne, kawai yayi ne don tserewa kai hari jiragen ruwa na Iran da makamai masu linzami. Manyan manazarta na Rystad Energy sun ce tankunan ajiyar mai a tashar jiragen ruwa na Farisa a halin yanzu suna a cike. Yayin da aka kwashe ma'aikatan jirgin ruwa saboda fargabar hare-hare, man da kasashen Larabawa ke hakowa ya ragu a tashoshin jiragen ruwa kuma ya kawo cikas ga fitar da shi zuwa kasashen waje.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha