14 Janairu 2026 - 21:18
Source: ABNA24
IRGC: Za Mu Mayar Da Cikakken Martani Ga Kuskuren Lissafin Makiya

Babban Kwamandan IRGC zamu bayar da martani ga kuskuren lissafin abokan gaba da yan hayarsa na ISIL. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Babban Kwamandan IRGC Pakpur a wani sako na jinjinawa al'ummar Iran na fitowarsu a taron jana'izar shahidai da aka gudanar a yau a Tehran ya tabbatar da cewa: Ba tare da kokwanto ba Trump da Netanyahu sune makasan jaruman samarin Iran da masu kare tsaronta.

Ayyukan taaddancin mai muni da yan hayarsu suka aiwatar ba za a taɓa mantawa da su ba, kuma a lokacin da ya dace zasu karbi sakamon hakan. 

Rundunar IRGC ta Jama'a masu ƙarfi suna kan kololuwar shirye-shiryen mayar da martani ga kuskuren lissafin abokan gaba da na cikin gida da yan hayar ISIL. 

Haɗin kai mai tsarki na al'ummar Iran ya warware shirye-shiryen yaudara na masu mulkin Fadar White House da Tel Aviv a kan Iran mai ƙarfi.

Your Comment

You are replying to: .
captcha