2 Janairu 2026 - 20:56
Source: ABNA24
Trump Da Netanyahu Suka Tsara Masu Zanga-Zangar Iran

Bayan batutuwan da Shugaban Amurka ya yi kwanan nan game da zanga-zangar da aka yi a Iran, wani jami'in Amurka ya sanar da cewa babu wani sauyi a yanayin tura sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya dangane da wannan batu.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wani jami'in Amurka ya ce sojojin kasarsa ba su sami umarni na shiga tsakani a cikin abin da ya kira "ceton masu zanga-zanga a Iran ba".

Al Jazeera ta ruwaito game da wannan batu: Jami'in Amurka ya ce babu wani sauyi a yanayin tura sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya dangane da zanga-zangar da aka yi a Iran.

Waɗannan kalamai sun zo ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump, a cikin wani rubutu a shafin "X", ya rubuta: "Idan Iran ta bude wuta kan masu zanga-zangar lumana ta kashe su da karfi - wani abu da suka saba yi - Amurka za ta shiga tsakani don ceton su".

Waɗannan kalamai na shiga tsakani sun jawo martani mai yawa daga jami'an Iran da sauran jama'a.

Baya ga masu fafutuka da mutane daban-daban, ciki har da Sakataren Majalisar Tsaron Kasa, Kakakin Majalisar Mohammad Baqer Qalibaf shi ma ya mayar da martani mai tsauri ga kalaman Trump ta hanyar cewa: "Da wannan Ikrarin a hukumance, dukkan cibiyoyin Amurka da dakarunta a yankin za su zama halaltattun abubuwan da za mu mayar da martani ga duk wani kasada da ka iya tasowa".

..........................

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha