30 Disamba 2025 - 21:37
Source: ABNA24
Saudiyya Ta Kai Hari Kan Wani Jirgin Ruwa Da Emerat Ta Aike Zuwa Dakarunta Da Ke Yemen

A cewar jaridar Middle East Eye, Saudiyya ta kai hari kan wani jirgin ruwa da Hadaddiyar Daular Larabawa ta aika zuwa ga sojojin da take marawa baya a Yemen a safiyar yau.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Riyadh ta sanar a wata sanarwa a hukumance cewa makamai da motocin da ke cikin jirgin "barazana ce ga tsaron Saudiyya".

Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta kuma sanar da cewa ta nuna rashin jin dadinta da ayyukan Hadaddiyar Daular Larabawa, wacce, a cewar ma'aikatar, ke matsa wa sojojin "Majalisar Canjin gwamanti a Kudancin Yamen" lamba don gudanar da ayyukan soji kusa da iyakokin Saudiyya. A karon farko, Saudiyya ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da goyon bayan kungiyoyin 'yan aware a Yemen.

Your Comment

You are replying to: .
captcha