Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Gwamnatin Zirin Gaza ta sanar da cewa yankin yana buƙatar gidaje kimanin 200,000 da aka riga aka gina domin biyan buƙatun agaji na gaggawa na 'yan gudun hijira da kuma tabbatar da cewa suna da ingantaccen masauki a lokacin da yanayi ke kara tsamama da tsauri.
Ƙungiyar Falasɗinawa ta ci gaba da cewa mummunan yanayin da ake ciki a yanzu ya haifar da nutsewa da lalata dubban tantunan 'yan gudun hijira a yankuna daban-daban na Zirin Gaza, wanda hakan ya ƙara yawan matsalar jin kai a yankin.
Your Comment