28 Disamba 2025 - 21:49
Source: ABNA24
Sheikh Naim Qassem: Amurka Da Isra’ila Su Ne Ke Haifar Da Rashin Kwanciyar Hankali

Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah a jawabinsa a lokacin cika shekaru biyu da rasuwar Hajj Muhammad Hassan Yaghi: Za mu tsaya tsayin daka, za mu yi tsayin daka kuma za mu cimma burinmu. Duk abin da makiya suka yi, ba zai taba kwace mana haƙƙoƙinmu ba.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sheikh Naim Qassem, Sakatare Janar na kungiyar Hizbillah a Lebanon, a jawabinsa a lokacin cika shekaru biyu da rasuwar Hajj Muhammad Hassan Yaghi, babban memba na kungiyar, ya bayyana cewa: Lebanon a yau tana cikin guguwa da rashin kwanciyar hankali saboda manufofin Amurka da maƙiyiya Sahyoniya.

Ya kara da cewa: Mamayar da Amurka ke yi kan hanyoyin tattalin arziki da dama na kasar ya kara ta'azzara lamarin sosai.

Sakataren kungiyar Hizbullah, yana mai jaddada cewa Tafarkin wannan kungiya yana da haske sosai, ya bayyana cewa: Hizbullah ta 'yantar da ba kawai kudancin Lebanon ba, har ma da dukkan Lebanon ne.

Sheikh Naim Qassem ya ce: Hizbullah tana lura da daidaito a mu'amalarta da gwamnati da jama'a kuma tana aiki a bayyane. Wannan motsi koyaushe yana taka rawa mai kyau wajen gina ƙasar da kuma aiki a cikin tsarin doka.

Da yake nuna cewa Lebanon na fuskantar wani sauyi na tarihi - ko dai ikon ƙasashen waje ko cikakken 'yanci - ya jaddada: Dole ne mu dawo da ikon Lebanon ta hanyar korar 'yan mamaye.

Kwace Makaman Gwagwarmaya; Makirci Ne Don Rusa Ikon Lebanon

Sheikh Naim Qassem ya ci gaba da cewa: Batun kwance damarar gwagwarmaya makirci ne na Isra'ila. Kwance damarar da ya kasance wani ɓangare ne na aikin lalata ikon Lebanon da kuma keta 'yancin ƙasar a kowane mataki.

Ya ƙara da cewa: Manufar wannan makircin ita ce kawo ƙarshen gwagwarmaya da mamaye sassan ƙasar Lebanon. Kamar yadda dalilin mamaye yankin Golan na Siriya da gwamnatin Sahyoniya ta yi shi ne rashin gwagwarmaya. Gwagwarmaya ce ta kori 'yan mamayar Sahyuniya daga Lebanon kuma ta wargaza makircin haɗa ƙasashen Lebanon da wannan gwamnatin.

Sheikh Naim Qassem ya ce: Gwamnatin Sihiyona ba za ta taba kwace filayen Lebanon ba saboda kasancewar masu adawa, kuma ba da jimawa ba za ta janye daga Lebanon saboda kasancewar masu adawa, gwamnati da jama'a.

Gwamnatin Sahyuniya Tana Karya Dokar Tsagaita Wuta

Sakataren Janar na Hizbullah ya ce: Gwamnatin Sahyuniya ba ta bin abinda tsagaita wuta ta tanada, yayin da gwagwarmaya ta bi yarjejeniyar; amma abokan gaban Sahyuniya suna ci gaba da kashe 'yan Lebanon da kuma kai hare-haren sama.

Da yake jawabi ga gwamnatin Lebanon, ya yi tambaya: Ina gwamnatin Lebanon take a gaban keta 'yancin kasar da abokan gaban Sahyuniya ke yi? Lokacin da abokan gaba ke ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, bai kamata a samu bin dokar yarjejeniyar ba daga bangare daya daga Lebanon ba.

Bai Kamata Gwamnati Ta Zama Mai Kare Tsaron Abokan Gaba Ba

Sheikh Naim Qassem ya jaddada cewa: Bai kamata a yi tsammanin gwamnatin Lebanon za ta taka rawar 'yan sanda don kiyaye tsaron abokan gaban Sahyuniya ba. Dole ne abokan gaba su janye gaba daya daga filayen Lebanon su kuma saki dukkan fursunonin Lebanon.

Ya kara da cewa: Mu ne ainihin masu Lebanon; Saboda haka, dole ne a dakatar da farmakin da ake kai wa wannan ƙasa, kuma dole ne maƙiyi Sahayoniya ta fice.

Sakatare Janar na Hizbullah ya ce: Za mu tsaya, za mu yi tsayin daka, kuma za mu cimma burinmu. Duk abin da maƙiyi ya yi, ba zai taɓa kwace haƙƙinmu ba.

Maƙiyi Ba Zai Iya Haifar Da Rashin Jituwa Tsakanin Mutane Da Gwagwarmaya Ba.

Sheikh Naim Qassem ya ce: Maƙiyi ba zai taɓa iya hana ci gaban mayaƙan gwagwarmaya ba, kuma kudancin Lebanon shine mafi kyawun shaida na wannan da'awar. Maƙiyi kuma ba zai iya haifar da rashin jituwa tsakanin mutane da gwagwarmaya ta hanyar haifar da cikas a kan hanyar sake ginawa ba.

Ya jaddada: Hizbullah da ƙungiyar Amal suna da ƙasa kwara ɗayauma za su ci gaba da kasancewa tare.

Warware Rikicin Ya Dogara Ne Da Cikakken Aiwatar Da Tsagaita Wuta Daga Gwamnatin Sahayoniya.

Sakataren Janar na Hizbullah ya kammala da cewa: Idan maƙiyi Sahayoniya da gaske yana son warware rikicin, dole ne ya aiwatar da tanade-tanaden yarjejeniyar tsagaita wuta gaba ɗaya.

Dukkan mutanen Lebanon suna buƙatar haɗin kai na magana don ceton ƙasar da ƙarfafa ikonta.

Ya jaddada: Hizbullah da Gwagwarmaya za su ci gaba da kasancewa masu daraja da ƙarfi, duk da duk wahalhalu da ƙalubale.

.........................

Your Comment

You are replying to: .
captcha