Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rundunar tsaron gabar tekun Amurka ta kwace jirgin mai mai suna "Bella 1" a cikin ruwan Tekun Atlantika. Jirgin ɗaukar man ba ya ɗauke da wani mai lokacin da aka dakatar da shi kuma yana cikin jerin jiragen da takunkuman Amurka ya shafa. Yunkurin rundunar tsaron gabar tekun na dakatar da jirgin ya fara ne a ranar Asabar da ta gabata, amma jirgin ya canza hanya ya nufi Tekun Atlantika.
Wannan matakin ya zo ne a matsayin wani ɓangare na matsin lambar da Washington ke yi wa fitar da man fetur na Venezuela. An riga an kwace wasu jiragen ruwa biyu, "Skiper" da "Centuries". Gwamnatocin Venezuela, Iran, Rasha da China sun yi Allah wadai da kwace jirgin, inda Caracas ta kira hakan da "fashin teku".
Your Comment