25 Disamba 2025 - 22:43
Source: ABNA24
Tsarin Kiwon Lafiya Ya Ruguje Gaba Ɗaya Yayin Da Isra'ila Ke Amfani Da Tsarin A Matsayin Makami.

Rahoton ya yi kira da a gaggauta shiga tsakani na ƙasashen duniya da kuma buɗe dukkan hanyoyin ketare iyaka ba tare da wani sharaɗi ba don ceton rayuka a Gaza.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jami'ai a Gaza sun yi gargaɗi game da wani bala'i na jin kai da na lafiya da ke tafe a yankin Zirin Gaza, suna cewa Isra'ila tana hana shigar da magunguna masu mahimmanci, kayan aikin likita, da mai da gangan, tana amfani da kiwon lafiya a matsayin makami ga fararen hula.

Ismail al-Thawabta, shugaban Ofishin Yaɗa Labarai na Gwamnati a Gaza, ya ce a ranar Alhamis cewa ɓangaren kiwon lafiya yana cikin mawuyacin hali ko a bayan tsagaita wuta - wanda ya fara a ranar 10 ga Oktoba - tare da ƙarancin magunguna, da kayan aikin likita.

Ya bayyana cewa saboda rashin maganin sa barci da kayan aiki masu mahimmanci, an dakatar da tiyata a asibitoci da yawa ko kuma gaba ɗaya. Ya yi gargaɗin cewa dakatar da tiyata yana sanya marasa lafiya cikin haɗarin mutuwa ko nakasa ta dindindin.

Al-Thawabta ya ƙara da cewa kusan tiyata 500,000 ne a halin yanzu aka dakatar, yayin da tsarin kiwon lafiya a Gaza ke fuskantar barazanar rugujewa gaba ɗaya. Ya ce, "A cewar gargadin Ma'aikatar Lafiya, lamarin yana da matuƙar tsanani kuma kusan ya tsaya cak," yana mai lura da cewa sauran asibitocin suna aiki fiye da ƙarfinsu saboda ƙarancin mai, ƙarancin ma'aikata, da kuma ƙarancin ƙarfin aiki.

Al-Thawabta ya jaddada cewa kayayyakin kiwon lafiya da ke shigowa Gaza ƙasa da kashi 10 cikin 100 na ainihin buƙatun kuma ana anfani da su nan da nan bayan isowa, ba tare da wani ci gaba mai ɗorewa a yanayin lafiya ba.

Ya nuna cewa Isra'ilawa "suna hana shigar da kayan aikin likitanci masu mahimmanci a ƙarƙashin dalilai na tsaro na ƙarya. Wannan manufar ta shafi amfani da magunguna da kiwon lafia a matsayin makami ga fararen hula".

Ya yi kira da a gaggauta shiga tsakani na ƙasashen duniya da kuma buɗe dukkan hanyoyin ketare iyaka ba tare da wani sharaɗi ba don ceton rayuka a Gaza.

Your Comment

You are replying to: .
captcha