25 Disamba 2025 - 22:14
Source: ABNA24
An Gargadi Isra'ila game da hatsarin Ƙaramin bam ɗin nukiliyar Iran

Wani jami'in Isra'ila ya yi gargaɗin cewa fafatawar soja da Tehran na iya zama dole idan Amurka ta gaza dakatar da shirin makami mai linzami na Iran.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jami'in Isra'ila Ya bayyana barazanar da makamai masu linzami na ballistic na Iran ke yi a matsayin mai tsanani kuma ya ce harba su da manyan makamai na iya haifar da lalacewa wacce yayi daidai da "ƙaramin bam ɗin nukiliya." Manyan jami'an Isra'ila sun riga sun kiyasta cewa za a iya kashe kuɗin yaƙin da Isra’ila ta yi da Iran a kan dubban biliyoyin shekel.

Your Comment

You are replying to: .
captcha