13 Nuwamba 2025 - 09:26
Source: ABNA24
Shugaban Afirka Ta Kudu: Rashin Halartar Amurka  Taron G20 Ya Nuna Shan Kayenta

Dangane da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa jami'an kasarsa ba za su halarci taron G20 da za a yi a Johannesburg ba, takwaransa na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce hakan shanke ne ga Amurkawa.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Ramaphosa ya shaida wa manema labarai cewa: "Za mu yanke manyan qudurori wanda rashin kasancewarsu yana nuna asararsu. Washington tana yin watsi da muhimmiyar rawar da ya kamata ta taka a matsayinta na babbar mai tattalin arziki a duniya".

Shugaban Amurka ya jaddada a cikin jawabinsa a ranar Juma'a cewa taron G20 da za a yi a Afirka ta Kudu abin kunya ne kuma babu wani jami'in gwamnatin Amurka da zai halarta.

Your Comment

You are replying to: .
captcha