3 Nuwamba 2025 - 11:04
Source: ABNA24
Sheikh Zakzaky: Isra'ila Na Amfani Da Matakin Tsagaita Wuta Ne A Matsayin Yaudara Kawai

Sheikh Ibrahim Zakzaky, shugaban Harkar Musulunci a Najeriya, ya soki gwamnatin Isra'ila saboda daukar yarjejeniyar tsagaita wuta a matsayin mara ma'ana, yana mai tabbatar da cewa ba za ta taba aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da Lebanon ko Gaza ba.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Sheikh Ibrahim Zakzaky, shugaban Harkar Musulunci a Najeriya, ya soki gwamnatin Isra'ila saboda daukar yarjejeniyar tsagaita wuta a matsayin mara ma'ana, yana mai tabbatar da cewa ba za ta taba girmama yarjejeniyar zaman lafiya da Lebanon ko Gaza ba.

Duk da tsagaita wutar da ake yi a yanzu, hare-haren sama na Isra'ila sun ci gaba da kai hari kan yankunan Gaza da kudancin Lebanon, wanda ya haifar da kashe daruruwan fararen hula, galibi mata da yara, tare da jikkata wasu da dama.

Tun lokacin da aka fara tsagaita wutar a ranar 10 ga Oktoba, kashi 20 cikin 100 na motocin agaji ne kawai aka bari suka shiga yankin Gaza, yayin da hare-haren bama-bamai na Isra'ila ke ci gaba da aukuwa. Masu sharhi sun bayyana cewa abin da ake kira tsagaita wutar da sojojin mamaye ke amfani da shi ne suna anfani da shi a matsayin dakatar da yaki domin su samu damar sake shirya kansu maimakon matakin gaskiya zuwa ga zaman lafiya.

Zakzaky ya jaddada cewa yanayin tarihi ya nuna yadda Isra'ila ta saba karya yarjejeniyar zaman lafiya.

Ya ce, "Duk wata yarjejeniya da sahyoniya kawai shed ace a takarda. Suna sanya hannu kan yarjejeniyoyi ne kawai don karya su a aikace".

A cewar Zakzaky, mamayar Isra'ila, wacce ta gaji da gazawarta a fagen daga, ta koma ga kisan gilla don tsawaita rikicin da kuma raunana 'yan adawa.

"Ba za ka iya kashe mutane tsawon shekaru da dama ba kuma ka yi tsammanin za su ajiye makamansu," in ji shi. "Tsayayya martani ne na halitta".

Da yake mayar da martani ga umarnin shugaban Lebanon Joseph Aoun na kwanan nan ga sojojin kasarsa su mayar da martani ga hare-haren Isra'ila, Zakzaky ya bayyana goyon bayansa.

"Wannan mataki ne mai kyau. Dole ne sojoji su kare 'yan kasarsu - ba wai su tsaya a tsaye ba yayin da ake yanka su. Muna fatan sojojin Lebanon da masu gwagwarmaya za su hada kai don kare kasarsu," in ji shi.

Masu nazari sun lura cewa kalaman Zakzaky suna nuna rashin amincewar yankin ga ayyukan da sojin  Isra'ila ke ci gaba da yi duk da ikirarin da aka yi na neman zaman lafiya. Rikicin jin kai yana ci gaba da tabarbarewa, yayin da kungiyoyin gwagwarmaya a Falasdinu da Lebanon suke ci gaba da kasancewa a tsaye – tafarkin da har yanzu siyasar Isra'ila ta kasa dakilewa.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha