3 Nuwamba 2025 - 08:42
Source: ABNA24
Kungiyoyin Falasdinawa Sun Yi Alƙawarin Yin Tsayin Daka Har Sai An 'Yantar Da Yankunan Da Aka Mamaye.

A ranar 2 ga Nuwamba, 1977, Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya na wancan lokacin, Arthur James Balfour, ya fitar da Sanarwar Balfour a cikin wata wasiƙa zuwa ga Lord Rothschild, shugaban ƙungiyar Zionist ta duniya, inda ya bayyana goyon bayan Birtaniya ga kafa Isra'ila a ƙasar Falasdinu.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Kungiyoyin gwagwarmaya na Falasdinawa sun bayyana Shelar Balfour, wadda ta kai ga kafa Isra'ila, a matsayin farkon jerin zalunci da laifukan da aka aikata wa al'ummar Falasdinawa da ƙasarsu.

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da aka fitar a ranar Lahadi, wacce ta cika shekaru 108 da shelanta Balfour, ƙungiyoyin Falasdinawa sun soki cibiyoyi da gwamnatocin da suka taka rawa wajen ƙirƙirar Isra'ila ba bisa ƙa'ida ba, suna masu cewa shirinta ya haifar da ƙaura da kuma take haƙƙin 'yan asalin ƙasar.

A cewar sanarwar, Amurka da ƙasashen Yamma, waɗanda ke da'awar kare haƙƙin ɗan adam, a zahiri suna taimaka wa gwamnatin Isra'ila mai mamaya ta ci gaba da jefa bama-bamai kasha yan kasa da kawanya da lalata gidajen Falasdinawa.

Sanarwar ta ƙara da cewa: "Ci gaba da rufe ido na siyasa na Yammacin duniya da kuma samar da makamai ga gwamnatin ya sake nuna haɗin gwiwarsu a kisan kare dangi da Isra’aila kewa Falasdinawa".

Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun tabbatar da cewa "Shelar Balfour" za ta ci gaba da kasancewa a cikin tunawa da al'ummar Falasdinawa da duk mutanen da ke son 'yanci, suna jaddada jajircewarsu da kuma ƙudurinsu na yin tsayin daka da duk wani shiri na korarsu ko kuma kawar da su.

Sanarwar ta ci gaba da yin kira da a samar da cikakken haɗin gwiwa da haɗin kai tsakanin dukkan ƙungiyoyin gwagwarmaya da ƙungiyoyi a Falasdinu don cimma 'yanci da 'yancin kai, tare da jaddada cewa wannan ita ce hanya ɗaya tilo ta cimma wani shirin ƙasa don sake gina Falasdinu da kuma mulkinta na gaba.

A wani ɓangare na sanarwarsu, ƙungiyoyin sun yi alƙawarin ci gaba da "juriya da gwagwarmaya ta kowace hanya" har sai an janye mamayar gaba ɗaya daga ƙasar Falasdinu.

A ranar 2 ga Nuwamba, 1977, Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya na wancan lokacin, Arthur James Balfour, ya fitar da Sanarwar Balfour a cikin wata wasiƙa zuwa ga Lord Rothschild, shugaban ƙungiyar Zionist ta duniya, inda ya bayyana goyon bayan Birtaniya ga kafa Isra'ila a ƙasar Falasdinu.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha