Sojojin Isra'ila sun kai hare-hare ta sama a yankin Nabatiyeh da Kafr Rumman a kudancin Lebanon. Sun kashe mayaka biyar na Hizbullah, ciki har da wasu daga cikin rukunin Rizwan na musamman An ce ɗaya daga cikin mayakan yana gyara cibiyoyin tsaro lokacin da aka kai hari.
Dubban mutane sun taru a Nabatiyeh don gudanar da jana'izar shahidai. An lulluɓe gawarwakin da tutocin Hizbullah (ja da rawaya) a cikin wannnan taro na nuna juriya mutane sun ta shelanta kalaman da sun haɗa da: "Kudanci ba zai mika wuya ba."
Mahaifiyar ɗaya daga cikin shahidai ta bayyana farin ciki da son ƙasa na ɗanta Labarin ya ba da ra'ayin cewa kowane shahidi yana ƙara ƙarfin juriyar al'umma.
            
            
                                        
                                        
                                        
                                        
Your Comment