1 Nuwamba 2025 - 14:50
Source: ABNA24
Al'ummar Yemen Sun Gudanar Da Muzahara Don Jaddada Ci Gaba Da Goyon Bayan Falasdinu

Yayin da barazanar da makiya na yanki da na Yahudawa ke yi wa Yemen ke ci gaba da gudana, birane da larduna daban-daban na ƙasar sun shaida zanga-zangar jama'a da mabanbantan qabiloli a yau.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Mahalarta taron, suna rera taken haɗin kai, gwagwarmaya, da cika alkawari ga shahidai, sun bayyana shirinsu na fuskantar duk wani makirci ko hari.

A lardunan Amran, Rima, Hajjah, Marib, Al-Mahwit, Taiz, da Al-Bayda, mutane suna ɗauke da hotunan shahidai kuma suna rera taken adawa da Sihiyoniya da Amurka, suna jaddada ci gaba da tafarkin jihadi, goyon bayan sojojin ƙasa, da goyon bayan al'ummar Falasdinu.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha