2 Nuwamba 2025 - 09:20
Source: ABNA24
Kasar Sin Ta Gabatar Da Shawarar Kafa "Kungiyar AI Ta Duniya"

A lokacin taron hadin gwiwar tattalin arziki na Asiya da Pacific (APEC), shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da shirin Beijing na kafa "Kungiyar AI ta Duniya."

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Shugaba Xi Jinping Ya ce manufar shirin ita ce samar da dokoki da tsare-tsare na kasa da kasa don gudanar da fasahar AI da kuma karfafa hadin gwiwa a duniya a wannan fanni.

Shugaban kasar Sin ya jaddada cewa AI ya kamata ta zama "albarkatu ga al'umma a duniya" ga dukkan kasashe, ba kayan aiki da wasu kasashe ke amfani da shi ba. A cewar jami'an kasar Sin, Shanghai ita ce babban zabi ga hedikwatar kungiyar.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha