Wani rahoton sirri daga Ofishin mai kula da Hanyoyin aiki na ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka (State Department Inspector General); ya bayyana cewa rundunonin sojin Isra’ila, sun aikata ɗaruruwan laifuka waɗanda za su iya zama keta dokokin kare haƙƙin ɗan Adam na Amurka yayin yaƙin da suke yi a Gaza. Abubuwan da ya kamata su haifar da dakatar da taimakon soji bisa dokar Leahy Law.
Wannan doka wacce ta ke kula da dokokin yaƙi ta hana Amurka bayar da taimako ga rundunar soji ta wata ƙasa idan an tabbatar da cewa ta aikata manyan laifukan keta haƙƙin ɗan Adam a wannan yaƙin da ta ke gabatarwa. Wani abun takaicu, duk da haka, duk da hujjojin keta haƙƙin ɗan Adam da suka zamanto a bayyane, na aiwatar da kisan kiyashi ciki har da kashe sama da Falasɗinu 100 a wani jerin gwanon rarraba tallafi a watan Fabrairu, da kuma harin da ya kashe ma’aikata bakwai na ƙungiyar World Central Kitchen a watan Afrilu, amma gwamnatin Biden ba ta dakatar da ko dalar taimako guda ɗaya ba da take taimakawa haramtacciyar ƙasar Isra'ila da shi ba.
Rahoton ya bayyana yadda Isra’ila ke samun tallafi cikin kulawa ta musamman, inda Washington ke buƙatar samun “ra’ayi ɗaya” a cikin gwamnati kafin a ɗauki matakin taƙaita taimako abin da ke zama wata ƙofa ta kauce wa hukunci domin kare mummunar ta'asar da haramtacciyar ƙasar Isra'ila ɗin ke aiwatarwa shekaru biyu da kwanaki a Gazza.
Masu suka sun ce, wannan ɓoyayyen tsari ne yana nuna yadda Amurka ke kare Isra’ila daga fuskantar hukunci, ko da tana aikata abubuwan da ke saɓawa dokokin da aka ƙirƙira domin hana Amurka shiga cikin laifukan yaƙi.
A yayin da masu sharhin al'amuran yau da kullum ke bayyana yadda Amurka ta zamanto kanwa uwar gami a yaƙin keta haƙƙin da Haramtacciyar ƙasar Isra'ila ke aiwatarwa a Gazza.
Haj Emaad
Your Comment