Yadda Isra'ila Ta Tsara Mamaye Duniya!

Ƙididdigar Ɓarnar Shekaru 2 Na Kisan Kiyashin Da Isra'ila Ke Yi A Gaza
31 Oktoba 2025 - 21:18
Source: ABNA24
Yadda Isra'ila Ta Tsara Mamaye Duniya!

Israel Shahak farfesa ne na ilimin sinadarai (organic chemistry) a Jami’ar Hebrew da ke Urushalima, kuma shi ne marubucin littafin “Shirin Siyonisanci Ga Gabas ta Tsakiya” (The Zionist Plan for the Middle East). A cikin wannan littafi, Shahak ya bayyana sirrin dabarun Siyonisawa na yadda suke shirin mallakar duniya ta hanyoyi da dama, wadanda suka haɗa da....

A yayin da kisan kiyashin da haramtacciyar ƙasar Isra'ila yake cika shekaru biyu da satikai, mun yi nazarin ɓarnar da ita da ta yi a ƙasar Falasɗinu. Ga dai abun kamar yadda Hukumar AJP ta Palastinu ta bayyana:-

A Ɓangaren Rayuka Gaba Ɗaya

1.Shahidai dubu 76.

2.An kashe Mahaifiya/Uwa guda dubu 9.

3.An kashe yaran da ba su wuce shekara ɗaya ba su dubu 10.

4.An kashe mace dubu 12,500.

5.An sace gangar jikin Shahidai 2,700.

6.Mutane dubu 9500 ba a san in da suke ba.

7.Mutane 2700 an shafe su daga kundin ƙididdiga .

8.Mutane 6200 kowanensu shi kaɗai ya tsira a cikin gidansu.

A Ɓangaren Ilimi

- An kashe Malamai 8900

- An kashe Dalibai 13,500.

- An rushe makarantu 670.

- An rushe Jami'o'i 338.

A Ɓangaren Abinci Da Harkar Noma

- An lalata gidajen gona 193.

- An lalata Gonakin shanu 97.

- An lalata ma'ajiyar Dawakai 94.

- Kaso 94/💯 na gonaki sun lalace.

- Hanyoyin ruwa kaso 90/100 an lalata su.

- Rijiyoyin da suke bayar da ruwa manya-manya guda 90 an lalata su.

Ɓangaren Wutar Lantarki

An lalata Turakun Lantarki guda 5080 da suke bayar da wuta.

Ɓangaren Wuraren Ibada

- An rushe Masallatai 835

Dangane Da Yaɗuwar Cututtuka A Tsakanin Palastinawa

- Mutum dubu 12500 ne suka kamu da cutar kansa.

- Mutum 1200 suka kamu da cutar makanta.

-Mutum 71 suka kamu da cutar hanta.

-Mutum 1200 suka kamu da shanyewar jiki.

Ɓangaren Asibitoci Da Motocin Da Aka Lalata

- Asibitoci 300 an rushe su gabaɗaya.

- Asibitoci 200 an lalata wani ɓangare na su.

Ɓangaren Muhallan Wasanni

- Gidajen ƙwallo 292 hare-haren ya lalata.

- 93 an lalata wani ɓangare na su

Yadda Isra'ila Ta Tsara Mamaye Duniya!

Israel Shahak farfesa ne na ilimin sinadarai (organic chemistry) a Jami’ar Hebrew da ke Urushalima, kuma shi ne marubucin littafin “Shirin Siyonisanci Ga Gabas ta Tsakiya” (The Zionist Plan for the Middle East). A cikin wannan littafi, Shahak ya bayyana sirrin dabarun Siyonisawa na yadda suke shirin mallakar duniya ta hanyoyi da dama, wadanda suka haɗa da:

1- Gina ƙarfi da ƙarfin tattalin arziki,

2- Haddasa rikice-rikicen fahimta tsakanin ƙasashe da al’ummomi,

3- Rarraba mutane bisa addinai, akidu, da mabambantan ra’ayoyi,

4- Haifar da rikice-rikice da yaƙe-yaƙe,

5- Yaɗa labaran ƙarya ta hanyoyin sadarwa kamar jaridu, rediyo, talabijin da kafafen sada zumunta,

6- Nishadantar da mutane don su manta da ainihin manufarsu ta rayuwa.

7- Mai da hankali kan wakoki, fina-finai, wasanni, da wasannin motsa jiki.

8- Tilasta wa malaman addini da sauran mutane yin biyayya ga manufofinsu.

Shekaru 75 da suka wuce, ƙasashen Turai karkashin jagorancin Amurka, Faransa, Ingila da kawayensu suka ƙirƙiri ƙasar Isra’ila ba bisa ƙa’ida ba daga cikin ƙasar Falasɗinu.

Tun daga wancan lokaci har yanzu, Siyonisawa suna ci gaba da kwace ƙasar Falasɗinu da kashe mutanen asali marasa laifi.

A ranar 7 ga Oktoba, 2023, dakarun Hamas suka kai hari domin ramuwar gayya kan dubban ’yan’uwa ’yan Falasɗinu da Siyonisawa suka kashe cikin shekaru 75 da suka gabata. Tun daga wannan lokaci har yanzu, Isra’ila ta ci gaba da kashe mata, yara ƙanana, tsofaffi, da lalata gine-gine, makabartu, da sauran wurare masu muhimmanci.

Bugu da ƙari, masu lura da harkokin duniya sun bayyana cewa, rushewar biranen Gaza da sauran yankunan Falasɗinu shi ne babban bala’in lalacewar gine-gine da aka taɓa gani a tarihin ɗan Adam.

Jaridar The Guardian da ke Birtaniya, ta buga labari daga Muna Shibli, inda ta bayyana cewa: “Akwai bincike da ya nuna cewa waɗanda za su rasa rayukansu saboda yunwa, ƙarancin ruwa, rashin magunguna, wahalhalu, da matsanancin yanayi a Gaza na iya kaiwa mutane 186,000.”

Haɗa rahoto:Haj Emaad

Tare da AJA-Palastine.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha