Indonesiya: Adadin Wadanda Suka Mutu Sakamakon Ruftawar Makarantar Ya Kai 54

Indonesia: Kungiyoyin Ceto Na Ci Gaba Da Kwashe Baraguzan Makarantu
6 Oktoba 2025 - 10:23
Source: ABNA24
Indonesiya: Adadin Wadanda Suka Mutu Sakamakon Ruftawar Makarantar Ya Kai 54

Hukumar yaki da bala'o'i a Indonesia ta fa da a yau litinin cewa adadin daliban da aka tabbatar sun mutu bayan ruftawar wani ginin makaranta a makon da ya gabata ya kai akalla 54 bayan da kungiyoyin agaji suka kwashe mafi yawan baraguzan ginin, waanna shine bala'i mafi muni da aka taba fuskanta a kasar a bana.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa:  Daraktan ayyuka na hukumar bincike da ceto ta kasar, ya shaidawa taron manema labarai cewa: "Mun gano gawarwakin mutane 54 da suka hada da ragowar mutane biyar," Yudhi Bramantyo,

Jami'an ceto na ci gaba da aiki ba dare ba rana domin gano wadanda suka bata. "Muna fatan kammala bincike a yau (Litinin) tare da mika gawarwakin" ga iyalai, in ji Yudhi.

Mataimakin darektan hukumar kula da bala'o'i ta kasar Budi Irawan, ya ce rugujewar ita ce bala'i mafi muni da aka taba samu a kasar Indonesia a bana. Ya kara da cewa akalla mutane 13 ne suka bata.

Your Comment

You are replying to: .
captcha