5 Satumba 2025 - 17:05
Source: ABNA24
Ministocin 5 Na Hizbullah Da Amal Sun Fice Daga Zaman Majalisa

Ministocin Hizbullah da na Amal sun fice daga taron gwamnatin Lebanon kafin su tattauna batun da ke da alaka da yadda gwamnati zata takaita mallakar makamai.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Bayan fara wani taro mai matukar muhimmanci na majalisar ministocin kasar Lebanon, wanda ake ganin zai yanke shawara kan makaman na Hizbullah. Ministoci 5 da ke da kusanci da kungiyoyin gwagwarmaya sun sanar da cewa zasu fice daga zaman majalisar idan har aka gabatar da shawarar kwance damarar Hizbullah bayan hakan kuwa sun tabbatar da ficewarsu bayan sanin cewa hukumar zata gabatar da batun kwance damarar Hizbullah din ne.

Sannan Hezbollah ta yi kira da cewa ya kamata gwamnatin Lebanon ta daina baiwa abokan gaba kai bori ya hau.

Bangaren Hizbullah a majalisar dokokin Lebanon: Daya daga cikin abubuwan da ake bukata na kare kasar Labanon da kuma kiyaye diyaucin kasa shi ne cewa gwamnatin Labanon ta sake yin la'akari da lissafinta ta daina ba makiya kai bori ya hau.

Kamata ya yi gwamnatin Lebanon ta sake yin la'akari da matakin da ta dauka na gaba gaɗi dangane da makaman gwagwarmaya.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha