Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Amin Sherry, amintaccen wakilin ga ɓangaren gwagwarmaya a Majalisar Dokokin Lebanon: Har yanzu muna cikin gwamnati kuma abin da ya faru shi ne kauracewa taron majalisar ministoci, ba janyewa faga gwamnati ba ne.
Muna bibiya da maida martani ga gwamnatin Nawaf Salam mataki-mataki.
Domin Matsin lamba da Amurka ke yi ga bangare daya ne kuma Washington ita ce babbar mai tsara shirin gwamnatin sahyoniyawa akan Lebanon da Siriya.
Kwamandan rundunar sojin kasar, Janar Rudolf Heikal, ya jaddada wanzar da zaman lafiya a cikin gida, kuma mu ma mun tabbata wajen wanzar da zaman lafiya, amma dole ne gwamnati ta sake duba lamarin.
Duk da haka. Gwamnatin Lebanon yarje da shirin takaita ga jami'an tsaro da sojoji kuma abinda ke cikin shirin sun bar shi a sirrance.
Ministan Yada Labarai na Gwamnatin Labanon a wani taron manema labarai bayan taron majalisar ministocin don kwance damarar dakarun gwagwarmaya ya ce: Majalisar ministocin kasar ta amince da shirin sojojin kasar na takaita mallakar makamai a kasar Lebanon. Mambobin gwamnati sun kuma yanke shawarar cewa abin da ke cikin shirin sojojin da tattaunawar da ke da alaka da shi za su kasance cikin sirri.
Your Comment