Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Har yanzu jami’an Iraqi ba su mayar da martani a hukumance kan lamarin ba. A baya dai an buga rahotannin karin motsin kungiyoyi masu dauke da makamai a yankunan kan iyakar Siriya da Iraki.
Birnin Bukamal yana gabashin lardin Deir Ezzor na kasar Siriya, kusa da iyakar kasar Iraki. Birnin ya kasance karkashin ikon kungiyar Nusra ne a lokacin yakin basasar Syria a shekara ta 2013 kuma bayan shekara guda ya fada karkashin ikon ISIS.
Your Comment