Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: ofishin hulda da jama’a na hukumar kare juyin juya halin muslunci ta Iran (IRGC) ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana harin da aka kai wa cibiyar tsara ayyukan ta’addanci na gwamnatin sahyoniyawan (Mossad) a birnin Tel Aviv.
Rubutun Sanarwa mai lamba 8 shine kamar haka:
بسم الله الرحمن الرحیم
فمن اعتدی علیکم فاعتدوا علیه بمثل ما اعتدی علیکم ...
سوره بقره (آیه ۱۹۴)
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai
Don haka duk wanda ya kawo muku hari, ku afka masa kamar yadda ya kawo muku...
Suratul Baqarah (aya ta 194).
Cikin yardar Allah Ta’ala a safiyar yau Talata 17 ga watan Yuni, mayakan IRGC Aerospace Force a wani aiki mai inganci, duk da kasancewar tsarin tsaro na zamani, sun afkawa cibiyar leken asirin soja na sojojin gwamnatin sahyoniyawa da ake kira Aman da cibiyar tsara ayyukan ta’addanci da munanan ayyukan gwamnatin sahyoniyawan (Mossad) a birnin Tel Aviv, kuma a halin yanzu wannan cibiya tana ci gaba da konewa cikin wuta.
Your Comment