Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Sardar Naeini, Kakakin IRGC: Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta nuna cewa kafafen yada labaran kasar suna da karfi da tasiri a fagen yaki. Muma Muna daukar kafafen yada labarai na kasa a matsayin abokan aikinmu.
Mintunan da suka gabata, an fara gabatar da jarin hare-hare kan Isra'ila, wannan harin hadakar makamai masu linzami da jirage marasa matuka. Wannan aiki yana ci gaba da gudana har zuwa wayewar gari.
Harin hadaka ne kuma muna amfani da dukkan bangarorin kuma ba za mu bari makiya su samu zaman lafiya ba. Ana gudanar da aikin ne tare da ƙarfin murkushewa da kuma wargazawa.
Your Comment