Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: wani makami mai linzami na kasar Iran ya kai hari a yankin Rishon Lezion da ke kudancin birnin Tel Aviv fadar mulkin yahudawan sahyuniya, lamarin da ya yi sanadiyyar lalata gine-gine da dama da kuma jikkata wasu da dama. Bisa labarin da aka bayar adadin wadanda suka mutu sakamakon harin makami mai linzami da Iran ta kai kan Rishon Lezion ya kai mutane 2 tare da raunata 38 daga cikin mutanen yahudawan sahyuniya, kuma an ce yanayin shida daga cikin wadanda suka jikkata na da muni.
Your Comment