16 Yuni 2025 - 18:22
Source: ABNA24
Kai Hari Ga Tehran Kaiwa Ne Ga Duniyar Musulmi, Musamman Pakistan/Martanin Mu Zai Zama Saran Takobin Haidar

Mataimakin shugaban majalisar hadin kan musulmi ta Pakistan ya jaddada a wani gangamin nuna goyon baya ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran cewa: Harin da ake kai wa Tehran wani hari ne ga kasashen musulmi musamman Pakistan.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: Hujjatul-Islam Sayyid Ahmad Iqbal Rizwi mataimakin shugaban majalisar hadin kan musulmin kasar Pakistan ya bayyana a wani gangamin nuna goyon baya ga jamhuriyar musulunci ta Iran da aka gudanar a yankin Kachora na Skerdo inda ya ce: “Kowa ya bar kasar Falasdinu ita kadai, amma mabiya Ali (AS) sun tsaya tare da ita. Harin da ake kai wa Iran wani hari ne ga al'ummar musulmi sannan kuma hari ne kan Pakistan.

Mataimakin shugaban majalisar hadin kan musulmi ta Pakistan ya yi gargadin cewa: Idan aka kai wa Tehran hari, su ma mazauna Islamabad ya kamata su damu.

Rizwi ya ci gaba da cewa: Gwamnatin yahudawan sahyoniyawa da ke cin karensu ba babbaka ba ta son Iran ta zama mai karfin nukiliya, kuma wannan lamari ne a sarari. A sa'i daya kuma, Isra'ila ita ce babbar abokiyar gabar nukiliyar Pakistan.

Ya ce: "A baya Yahudawa sun kalubalanci Sayyidina Ali (AS) a Khyber, kuma sun sha kashi, a yau ma sun kalubalanci dan Ali (AS) Sayyid Ali Khamene'i, kuma in sha Allahu za a sake samun galaba a kan makiya." Mataimakin shugaban majalisar hadin kan musulmin Pakistan ya kara da cewa a karshe: "Sun kai hari ne kwara daya, amma martaninmu da zamu mayar zai kasance saran takobi daya na Haidar".

Your Comment

You are replying to: .
captcha