Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: majiyoyin Labarai sun sanar da fara kai hari da makami mai linzami na Iran ga Isra'ila .
Kafofin yada labaran sun ce akwai yiwuwar shigar Yemen cikin harin da Iran ke kaiwa a yanzu.
Kafofin yada labaran Isra'ila: Rahotanni na nuna cewa an harba makamai masu linzami kusan 70 daga Iran.
Kamfanin samar da wutar lantarki na Haifa na ɗaya daga cikin hadafin wannan harin inda ya samu rabansa shi ma da saukar gungun na makaman anga wuta na tashi bayan saukar makamai masu linzami na Iran.
Waɗannan makamai sun isa yankunan daban-daban da aka mamaye
Biyo bayan hakan an samu afkuwar katsewar wutar lantarki a tsakiyar Isra'ila.
A wannan harin Sojojin Isra'ila sun ce kusan rokoki 100 na Iran aka harba wa Isra'ila a harin
Gidan rediyon sojojin Isra'ila ya bayar da rahoton cewa, bisa ga shedun gani da ido, makaman Iran din sun afkawa yankuna uku na Tel Aviv.
Your Comment