15 Yuni 2025 - 18:51
Source: ABNA24
Iran Ta Sake Kai Harin Kan Gidan Netanyahu Da Wasu Muhimman Wurare A Karo Na Uku Na Maida Martani.

Gidan rediyon sojojin Isra'ila, ya nakalto majiyar sojin Isra'ila, ya tabbatar da harba makamai masu linzami fiye da 50 daga kasar Iran, kuma an yi ta jin karar kararrawa a duk yankunan da aka mamaye Mutane sama da 500 suka jikkata 12 suka sheka lahira.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: a ci gaba da mayar da martani mai tsanani da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take yi kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, wasu sa'o'i kadan da suka gabata ne aka fara kai wani sabon hari da makami mai linzami da Iran ta yi kan yankunan da aka mamaye. An harba manyan makamai masu linzami na ballistic daga sassa daban-daban na kasar Iran zuwa wasu muhimman wurare a Palastinu da aka mamaye, an kuma bayar da rahoton tashin bama-bamai a garuruwan Kudus, Tel Aviv da Haifa.

Majiyoyin labarai sun sanar da cewa garuruwan Ashkelon, Tel Aviv da Haifa suna ciki tsundum a wadannan hare-haren. Tashar talabijin ta Isra'ila ta Channel 12, ta tabbatar da munin hare-haren, ta bayar da rahoton wasu bama-bamai da aka kai a birnin Kudus da ke mamaye, tare da bayyana yanayin da ake ciki a wannan birni a matsayin mai matukar tsananin wahala.

Da yake tsokaci daga majiyoyin soji, gidan rediyon sojojin Isra'ila ya tabbatar da harba makamai masu linzami fiye da 50 daga kasar Iran, kuma an yi ta kara ta jin karara a cikin yankunan da aka mamaye. Wadannan hare-haren sun kalubalanci tsarin tsaron Isra'ila, wanda shekaru da yawa suka yi ikirarin cewa ba za su iya shiga ba.

Kafofin yada labarai na yaren yahudanci sun bayar da rahoton cewa, an kai harin ne a gidan firaminista Benjamin Netanyahu mai laifin ta'addanci da kuma tashar wutar lantarki ta Khudaira. Wannan mataki wani sako ne karara ga jagororin gwamnatin ‘yan mamaya na cewa babu wani bangare na yankunan da aka mamaye da ya tsira daga karfin makamai masu linzami na Iran da kuma ‘yan gwagwarmaya.

Ana gudanar da wannan gagarumin aiki ne a daidai lokacin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta shafe shekaru tana jefa zaman lafiyar yankin cikin hadari tare da munanan ayyukanta da suka hada da kai hare-hare kan al'ummar Palastinu da ake zalunta da keta hurumin kasashen yankin. Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sha nanata cewa duk wani wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila za ta yi za ta fuskanci murkushewa masu tsauri cikin azama.

A yayin da aka fara kai hare-hare, kafafen yada labaran yahudawan sahyuniya sun tabbatar da cewa wannan shi ne karo na farko da Iran ta kai hari da rana tsaka, kuma wannan lamari ne babba mai hatsarin gaske.

A cewar wani rahoto da wakilin Al-Hadath ya bayar daga bayanin farko kan hasarar rayuka da harin makami mai linzami na Iran ya yi, a cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta Isra'ila, an jikkata Isra'ilawa 500, yayin da mutane 12 suka mutu ya zuwa yanzu.

Your Comment

You are replying to: .
captcha