Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: Sayyid Ammar Hakim, jagoran kungiyar Hikima ta kasa, a wani taro da wasu kabilun kasar Iraki suka gudanar a birnin Bagadaza ya jaddada cewa, kasar Iraki ba wai tana cikin tsaka-tsaki ba ne a yakin da ake yi tsakanin kasar Iran da gwamnatin sahyoniyawa, sai dai tana goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne.
Sayyid Ammar Hakim ya lissafta wannan goyon baya da tallafi ga Jamhuriyar Musulunci ga Iran a fannoni daban-daban na siyasa, diflomasiyya, yada labarai da jin kai.
Wannan shugaban siyasar Irakin ya yi nuni da cewa, nasarar da Iran ta samu wajen tunkarar gwamnatin sahyoniyawa abin farin ciki ne da jin dadi. Ya ce, duk da irin sassauci da kau da kai da ta nuna a tattaunawar nukiliyar, amma Iran ta fuskanci wuce gona da iri daga abokan gaba.
Your Comment