Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ma'aikatar ta kara da cewa, jami'an ceto sun kuma kwashe gawarwakin shahidai 6 daga karkashin baraguzan ginin tare da kai su asibiti. Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a zirin Gaza ta sanar da cewa, tun daga ranar 18 ga watan Maris din da ya gabata, lokacin da gwamnatin mamaya ta keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza, Falasdinawa 5,194 ne suka yi shahada yayin da wasu 17,297 suka jikkata.
Don haka adadin shahidai a yakin kisan kare dangi na Isra'ila a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ya karu zuwa 55,493 kuma adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa 129,320. Sama da mutane 10,000 ne har yanzu ba a gan su ba a zirin Gaza da ke karkashin baraguzan ginin.
Your Comment